An kashe mutum 1 da yin garkuwa da wasu 5 a Neja




A wani sabon hari rahotanni sun ce an kashe wani manomi ɗaya yayin da wasu ’yan bindiga suka sace wasu biyar a Tungan-Gari da ke Ƙaramar hukumar Kontagora a gundumar Neja ta Arewa a jihar Neja.

Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, ’yan bindiga sun kai wa al’ummar garin hari ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Alhamis inda suka yi ta harbe-harbe na tsawon sa’o’i ba tare da an ƙalubalantarsu ba.

Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su akwai mata huɗu da namiji ɗaya.

“Ba mu da wani zaɓi a yanzu da ya wuce mu tashi mu kare garuruwanmu da al’ummarmu, duk wanda ya jira matakin gwamnati a yanzu ya yi wa kansa ne.

Allah Ya duba halin da muke ciki ya kawo mana ɗauki, yawancin mutanenmu sun kwashe makonni suna tare da ’yan bindiga,” in ji ɗaya daga cikin mazauna yankin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun bai mayar da martani ga saƙon da aka aika a wayarsa ba, yayin da lambarsa ta ƙi shiga lokacin da wakilinmu ya kira shi.

Daily Trust ta samu rahoton cewa waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar Ilimi bai ɗaya ta Jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo da Kwamishinonin dindindin su  bakwai na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja, Barista Ahmad Mohammed sun buƙaci a biya su Naira miliyan 300 kafin a sako su.

Wata majiya ta kusa ga iyalan ta ce, iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su na kokawa da neman agaji domin a sako ’yan uwansu.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *