Wani Direba Da Ya Buge Mai PoS Har Lahira Ya Tsere A Abuja
[ad_1]
Wata mata mai sana’ar (POS) ta rasu bayan da wata motar bas ta haya ta buge ta a kusa da gidan mai na Total da ke yankin Berger a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Shaidun gani da ido sun ce direban bas din, wanda ke tukin bas ta kasuwa, yana tserewa ne daga jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) lokacin da lamarin ya faru.
- An Nada Liu Xianfa Wakilin Musamman Na Gwamnatin Sin Kan Harkokin Afirka
- Bayan Jinkiri Da Dimbin Hasashe Abba Kabir Yusuf Ya Rungumi Tafiyar Tinubu
Wani fasinja da lamarin ya faru a gabansa, mai suna Johnson, ya shaida wa wakilinmu cewa matar ta zo aiki da sassafe ta zo tsallaka titi bayan ta sayi abinci. Ya kara da cewa bayan motar bas ta buge ta, ba direban bas din ko jami’an FRSC suka tsaya a wajen ba.
Ya ce: “Matar da aka kashe mai POS ce a yankin. Ta zo da sassafe, ta je ta sayi abinci, tana kokarin tsallaka titi a kusa da gidan mai na Total, sai ga jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) na bin wata motar coaster bas da gudu. A wannan lokaci, bas din ya buge matar ya jefa ta zuwa daya gefen hanya.”
Ya ci gaba da cewa: “Direban bai tsaya ba. Motar FRSC ma ba ta tsaya ba. Sun ci gaba da bin bas din da gudu sosai. Gawar matar ta jima a kan hanya tare da mummunan rauni. Matar ta rasu kafin jami’an ‘yansanda daga sashen Utako su iso. Wani mutum ya dauki bidiyon duk abin da ya faru ya nuna wa ‘yansanda. Na gan shi yana tafiya tare da su,” in ji Johnson.
Wani mai sayar da jaridu a yankin ya tabbatar da cewa lamarin ya faru da safe a kusa da gidan man Total, yana mai cewa motar bas din da ta buge matar da kuma motar FRSC sun ci gaba da tafiya bayan hadarin.
Wani mai POS a yankin, Ola, ya ce jami’an FRSC suna yawan bin motoci da gudu a yankin. Ya tuna wani makamancin lamari da ya faru a ranar Asabar da ba a samu asarar rai ba saboda karancin jama’a a wancan lokaci.
Ya ce: “A nan ne lamarin ya faru. Jami’an FRSC suna yawan yin irin wannan bin motoci a nan. A ranar Asabar sun bi wata motar coaster bas, a ranar da aka samu cunkoso kamar Litinin, da hakan ya iya kashe wani. Wannan ba shi ne karo na farko da suke bin motoci a wannan wuri ba. Watakila idan muka sake ganinsu a nan, za mu kore su,” in ji shi.
Kwamandan FRSC na FCT, Felid Theman, ya ce hukumar na gudanar da bincike kan lamarin. A cewarsa, an kira dukkan tawagogin sintiri da ke aiki a Central Area, Zone 7, da yankunan da ke makwabtaka domin tantance ko wace motar FRSC ce ta shiga lamarin.
Ya ce: “Na samu rahoto makamancin wannan, kuma a halin yanzu muna bincike. Na kira dukkan tawagogin sintiri, musamman a Central Area, Zone 7 da kewaye, domin gano ko da gaske wata motar sintirinmu ce ta shiga lamarin. Da zarar bincikenmu ya tabbatar da gaskiya, za mu fitar da sanarwa ga manema labarai.”
Ya kara da cewa: “A halin yanzu muna dubawa ne domin tantance sahihancin lamarin. Amma mun san cewa a lokuta da dama, ko da ina amfani da motar aiki kawai, idan wani ya aikata laifi ko ya ketare dokar hanya, mutane kan dauka cewa ana kokarin kama su. Wani lokaci har su kan tare mota, ko da ba a gudanar da sintiri ba.”
Ya ce mutane da yawa ba sa bambance motar sintiri da sauran motoci, yana mai cewa wasu motocin daukar kaya (pickups) ana amfani da su ne don wasu ayyuka daban, ba lallai don sintiri ba.
Ya kammala da cewa: “Har sai mun tabbatar ko da gaske tawagar sintiri ce ke bin wani, zai yi wuri mu ce jami’an sintiri ne ke binsa. Haka kuma na san cewa wannan yanki na da yawan cunkoso sosai.”
[ad_2]
Source link