IS Ta Fitar Da Bidiyon Harin Da Ta Kai Kan Sansanonin Soji A Yamai

[ad_1]

Kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS ta fitar da wani sabon faifan bidiyo, wanda ke nuna irin barin wutar da ta yi a harin da ta kai kan sansanin sojin sama a babban birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Kamfanin dillancin labarai na Amak ne ya yada faifan bidiyon, kafar yada labaran da ake ganin na yada farfagandar kungiyar ta masu tayar da kayar baya.

  • Xi Ya Mika Gaisuwar Bikin Bazara Ga Tsoffin Sojojin Sin
  • Babban Sakataren AL Ahmed Aboul Gheit: An Sada Zumunta Mai Zurfi Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa

Sojoji hudu ne suka samu raunuka, inda jiragen sama da dama suka lalace a harin da aka kai filin jirgin saman ranar Alhamis.

Bidiyon ya nuna fashewar wani abu a bangaren ajiyar jiragen sama masu saukar ungulu, inda aka nuna yadda wani jirgin sama yana ci da wuta, yayin da harbin bindiga ya lalata jiragen dakon fasinja da dama.

Filin jirgin saman Yamai tamkar wata cibiya ce mai muhimmanci wacce ke dauke da sansanonin sojoji, hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta Niger da Burkina Faso da Mali, da kuma wani babban rumbu mai ajiye da makamashin Uranium wanda ake takaddama akansa da kamfanin Orano na Faransa.

Gidan talibijin din gwamnati ya ruwaito cewa sojoji sun yi gaggawar mayar da martani a lokacin harin, abin da ya basu damar kashe mahara 20 tare da kama 11 daga cikinsu.

A bara, mayakan da ke samun goyon bayan al-Kaeda da IS sun tsaurara kai hare-harensu a sassan Sahel, lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Nijar ta kasance abokiyar wasu kasashen Yammaci, kafin daga bisani ta sauya akala bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a 2023. Tun daga lokacin ne gwamnatin mulkin sojan ta yanke hulda da Faransa, tare da karkata alkiblarta zuwa ga Rasha, domin  taimaka mata wajen yakar masu tayar da kayar baya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *