Shin Ko Lokacin Lashe Firimiyar Arsenal Ya Yi?
[ad_1]
A halin da ake ciki kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayar da tazarar maki 9 tsakaninta da Manchester City, yayinda take matsayi na daya a saman teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila bayan buga wasan mako na 25.
Fiye da shekaru 20 kenan rabon da kungiyar dake birnin Landan ta lashe gasar Firimiya, a shekarar 2005 Arsenal ta samu nasarar lashe gasar ba tareda rashin nasara ko daya ba.
- An Yi Taron Share Fage Na Shirin Talibijin Na CMG Na Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa A Addis Ababa
- Kasuwar Musayar ‘Yan Kwallo: Yadda ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Canza Kungiyoyi
Duk da cewa kungiyar ta sha barar da damarmakin da ta samu na lashe gasar a shekaru biyu da suka gabata, amma a halin da ake ciki kungiyar wadda Mikel Arteta ke jagoranta ta cigaba da zage damtse wajen ganin ta faranta ran miliyoyin magoya bayan da take dasu a fadin Duniya.
Arsenal ta hada maki 56 da kwallaye 32 a wasanni 25 da ta buga, hakazalika ta samu nasara sau 17 ta buga canjaras 5 sannan aka doke ta sau 3 a wannan kakar da muke ciki.
Ba’a iya gasar Firimiya Arsenal ke kan teburi ba har ma da gasar zakarun Turai inda ta kare zagayen farko na rukuni a matsayi na daya, duba da cewa kungiyar ba ta taba lashe gasar zakarun Turai a tarihinta ba, wannan babbar dama ce gareta wajen ganin ta baiwa marada kunya.
[ad_2]
Source link