Kasashe 10 Da Kudadensu Suka Fi Daraja A Duniya

[ad_1]

Duk da cewa Dalar Amurka ne kudin da aka fi hada-hada da shi, amma hakan bai sa ya zama mafi daraja ba a duniya.

Mujallar Forbes ta fitar da jerin kudin kasashe 10 mafiya daraja a duniya, inda aka yi amfani da wani ma’auni bisa ga bayanai da aka tattara a kasuwar hada-hadar canjin kudaden duniya.

  • Kasuwar Musayar ‘Yan Kwallo: Yadda ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Canza Kungiyoyi
  • Garkuwa: TETFund, NSCDC Sun Hada Gwiwa Don Magance Tsaro A Makarantu

Dinar Kuwaiti

Ta hanyar amfani da wannan ma’auni, an gano cewa Dinarin Kuwait ne kudi mafi daraja a duniya, inda ake sayar da Dinari daya kan Dala 3.25.

A takaice, a misali za a iya cewa Dalar Amurka daya daidai take da kobo 30 na Dinarin.

Kuwait dai na tsakanin kasashen Saudiyya da Iraki, inda take samun yawan kudaden shigar ta daga fitar da danyen man fetur.

Dinarin Bahrain

Dinari daya na Bahrain ya kai Dala 2.65. Hakan ya sanya Dala zama, misali a kobo 37 na kudin kasar.

Bahrain kasa ce da ke yankin Gulf, inda take iyaka da gabar tekun Gulf da kuma Saudiyya a daya gefen.

Kasar dai na samun kudadenta daga bangarori da dama, inda abubuwan da take samu wanda ba shi alaka da mai ya kai kashi 85.9 a 2024.

Riyal in Oman

An fara amfani da Riyal din Oman a 1970. Riyal daya ya kai akalla Dalar Amurka 2.60.

A takaice, a misali za a iya cewa Dalar Amurka daya daidai take da kobo 38 na kudin Oman.

Kasar na makwabtaka da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Yemen.

Oman na cikin sahun gaba a kasashen duniya da ke fitar da man fetur da iskar gas, kamar sauran makwabtanta masu arziki.

Dinarin Jordan

Dinarin na Jordan wanda aka fara amfani da shi a shekarun 1950, ya kai darajar Dala 1.41, inda yake matsayi na hudu a jerin kudade mafiya daraja a duniya.

Jordan kasa ce da ke yankin Gabas Ta Tsakiya. Ba ta dogara sosai da man fetur ba kamar sauran makwabtanta.

Sai dai, kasar ta fuskanci matsalar tattalin arziki da kuma karuwar basuka.

Fam Na Ingila

shi ne tushen tushe.

An fara amfani da fam din Gibraltar ne a shekarun 1920, kuma a yau ana alakanta darajarsa da ta fam din Ingila, abin da ke nufin zai ci gaba da tafiya daidai da fam din Birtaniyar.

Gilbraltar wani yanki ne da ke karkashin Birtaniya a kudancin Sifaniya.

Franc da Switzerland

Franc shi ne nau’in kudi da Switzerland da kuma Liechenstein ke amfani da shi a hukumance.

Kuma ana daukar kudin a matsayin wanda ba shi da barazanar durkushewa saboda yadda tsarin siyasar Switzerland ke tafiya cikin tsanaki.

Franc din ya fara wanzuwa ne a shekarar 1850. Franc daya na Switzerland daidai yake da Dala 1.24.

Dalar tsibirin Cayman

Tsibirin Cayman wani yankin Birtaniya ne a yankin Carribbean, kuma an fi sanin yankin kan irin damar da yake bai wa dukkan mutane.

An fara amfani da Dalar Cayman ne a shekarun 1970, kuma ana alakanta ta da Dalar Amurka.

Ana canja Dalar Cayman daya zuwa Dalar Amurka 1.24.

Kudin Yuro

A shekarar 2002 aka fara amfani da Yuro a hukumance.

Kudi ne da kungiyar kasashen Turai ke amfani da shi, inda kasashe akalla 20 cikin 27 ke mu’amala da kudin.

Ana canja yuro daya kan Dalar Amurka 1.16.

Dalar Amurka

Dalar Amurka ta samu shiga cikin jerin kudaden kasashe 10 mafiya daraja a fadin duniya, .

An fara amfani da kudin ne a shekarun 1700, kuma shi ne aka amince da shi a kasar, har da wasu yankuna da kuma kasashe masu cin gashin kai – ciki har da Ecuador.

Tattalin arzikin kasar Amurka shi ne mafi girma a duniya idan aka yi la’akari da tattalin arzikin cikin gida (GDP) – kuma Dalar ita ce wadda aka fi hada-hada da ita a fadin duniya.

An kuma fi amfani da kudin Dala wajen cinikayya a kasuwanni, musamman wajen sayen mai, da zinare da kuma ma’adinai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *