Kasuwar Musayar ‘Yan Kwallo: Yadda ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Canza Kungiyoyi
[ad_1]
‘Yan wasa da dama daga Nijeriya, sun samu sauyin kungiyoyin da suke taka leda, yayin da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta nahiyar Turai.
A watan Janairu, yayin da wasu suka canza kungiya a matsayin aro, wasu kuma sun canza ne a matsayin dindindin.
- Shugabancin Ƙungiyar Kasuwar Singa (SIMDA) Ya Karyata Rahoton Tashin Sabuwar Gobara A Kasuwar
- Arewa Maso Gabashin Jigawa: Abokan Babandede Sun Dauki Harama
Leadership Hausa, ta zakulo muku cikakken jerin sauye-sauyen kungiyoyin da ‘yan wasan suka samu.
ADEMOLA LOOKMAN
Atalanta zuwa Atletico Madrid (Yuro Miliyan 35)
Daya daga cikin manyan canje-canjen da aka samu shi ne, sauya shekar dan wasan Atalanta, kuma tsohon gwarzon dan kwallon kafar nahiyar Afirika.
Ademola Lookman, wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta kasar Sifaniya, a kan kudi Yuro miliyan 35.
Lookman ya taka rawar gani a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirika da aka kammala a Kasar Morocco, bayan ya zura kwallaye 3, kuma ya taimaka wajen zura 4, hakan ya kara habaka martabarsa a fagen kwallon kafa a duniya, wanda ya jawo Atletico Madrid ta biya Yuro miliyan 35, domin daukar dan wasa mai shekaru 28, Lookman ya zama dan wasa na biyu daga Nijeriya da zai buga wa Rojiblancos din wasa a tarihi.
FRANK ONYEKA
Brentford zuwa Cobentry City (Aro)
Wani sauyin sheka da ya bayar da mamaki shi ne, na Frank Onyeka, wanda kungiyar Brentford ta bayar da shi aro ga Cobentry City da ke buga gasar Championship ta Kasar Ingila, amma Onyeka yana da damar taka muhimmiyar rawa a kokarin da Cobentry City ke yi, wajen ganin sun samu gurbi a gasar Premier League a karon farko cikin shekaru 25.
BICTOR MUSA (Fc Kaysar)
Bayan shafe wata bakwai ba tare da kungiya ba, Moses dan shekara 35,
ya sanya hannu a wani kwantiragi da kungiyar kwallon kafa ta FC Kaysar ta kasar Kazakhstan, tsohon dan wasan na Chelsea, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara daya, inda ake fatan zai taimaka wajen mayar da kungiyar da ke fama da kalubale zuwa matakin nasara.
WILLIAM TROOST-EKONG
Al-Kholood zuwa Al-Ahli
Tsohon kyaftin din Super Eagles, ya samu canjin kungiya babu zato babu tsammani a watan Janairu, Ekong ya bar tsohuwar kungiyarsa ta Al-Khoolod ta Kasar Saudiyya, inda ya koma kungiyar Al-Ahli ta kasar Katar, inda nan take ya lashe gasar cin kofin UAE (Katar Super Cup), bayan samun nasara a kan Al Jazira.
SAURARA (Biki)
Dan wasan tsakiya mai shekara 27, ya sha fama da rashin buga wasanni a Southampton, a wannan kakar ta bana, hakan ya sa ya zabi komawa Leicester City a matsayin aro, inda ake ganin wannan canjin da ya samu zai zamar masa wata hanya da zai nuna wa duniya irin bajinyar da yake da ita a fagen taka leda.
SADIQ UMAR
Real Sociedad zuwa Balencia (Yuro miliyan 5)
Sadik ya kawo karshen wahalar da ya sha a Real Sociedad na rashin samun lokutan wasanni, bayan komawa Balencia a zaman dindindin na kungiyar da a baya ya zauna zaman aro, yanzu dan wasan yana da sabuwar dama ta farfado da kwarewarsa da kuma sake samun tagomashi a bangaren wasannin gida.
ZAUREN MOFFI
OGC Nice zuwa Fc Porto
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Terem Moffi da magoya bayan Nice a
kwanakin baya, inda har ta kai ga magoya bayan kungiyar sun jefi dan
was an, bayan wata rashin nasara da suka yi, hakan ya sa tsohon dan wasan tawagar Super Eagles din ya zabi komawa Fc Porto a matsayin aro, dan wasan zai yi kokarin ganin zaman aron ya rikide zuwa zaman dindindin.
RAFIU DUROSINMI
Gidan zoo na Bytoria Plz ( Yo 9 mil)
Dan wasan gaban mai shekara 23, ya kammala komawa kungiyar Pisa da ke buga gasar Serie A ta Kasar Italiya ba tare da wata matsala ba a farkon watan Janairu, Durosinmi ya samu nasarar jefa kwallo 1, kuma ya taimaka aka jefa kwallaye 3, tun bayan komawarsa Pisa.
TOCHUKWU NNADI
Zulte Waregem zuwa Marseille (Yuro miliyan 6)
Dan wasan tsakiya mai shekara 22, yana cikin tawagar Nijeriya ta AFCON na 2025 da aka kamala, a cikin tawagar ‘yan wasan na tsakiya, ya ci gaba da samun ci gaba cikin sauri a harkar kwallon kafa, ana kallonsa a matsayin wanda zai iya maye gurbin Wilfred Ndidi, komawar Nnadi zuwa babbar kungiyar Ligue 1 ta Marseille, alama ce ta samun babban ci gaba.
SALIM FAGO LAWAL
NK Istra zoo Biktoria Plzen (2 miniinn 2)
Shigar Salim Fago cikin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, ta bai wa
kungiyarsa ta Istra mamaki, kwallaye 7 da ya ci, kuma ya taimaka wajen
jefa 2, wadanda suka taimaka wa Istra zuwa matsayi na 3 a teburin gasar kasar.
Croatia, komawarsa zuwa Bictoria Plezn, zai zama wani mataki babba a
rayuwarsa ta kwallon kafa, yayin da kuma zai sake samun gayyata daga
tawagar kasa.
LEONARD BA TARE
Remo Stars zuwa Leeds United
Dan wasan mai shekara 18, ya samu ci gaba mai girma daga gasar kwallon kafa ta Nijeriya zuwa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Ingila, duk da cewa; a halin yanzu ya shiga makarantar horar da ‘yan was an Leeds United, wannan wata alama ce da ke nuna kyakkyawar makoma ga dan wasan.
CHIBUIKE MATA
Wolfsberger zuwa Trabzonspor (Yuro miliyan 5)
Dan wasan tsakiya mai shekara 22, ya sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Trapzanspor ta kasar Turkiyya, inda ya buga wasanni uku zuwa yanzu a gasar, tun bayan komawarsa a watan Janairu, tsohon dan wasan na Enyimba ya bayyana a shirye ya ke wajen ganin ya samu wuri a kungiyar.
Sauran su ne:
UCHENA OGUNDU
Alanyaspor zuwa Augsburg (Yuro miliyan 4)
SULEMAN SANI
Trencin zuwa RB Leipzig (Yuro miliyan 5)
ahije shine ma’auni
Sheffield United zuwa Atromitos (Aro)
SOJOJIN OPARA
Nobi Pazar zuwa Biktoria Guimaraes
[ad_2]
Source link