Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ko maudu’in wannan taron, wanda shi ne karo na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da shugaban ƙasar ya yi.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce taron ba zai nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunar sojoji a ƙasar nan ba.

Tinubu yayin ganawa da sabbin hafsoshin tsaro

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron ƙasar, a wani sauyi a tsarin jagorancin sojin ƙasar domin inganta da ƙarfafa sha’anin tsaro a Najeriya.

Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.

Sabbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya nada sun hada da Janar Olufemi Oluyede — Hafsan Hafsoshi da Manjo Janar W Sha’aibu — Hafsan sojojin ƙasa da Air Vice Marshall S.K Aneke — Hafsan sojin sama.

Akwai kuma Rear Admiral I. Abbas — Hafsan sojin ruwa da Manjo Janar E.A.P Undiendeye — Shugaba sashen tattara bayan sirri na soji.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *