Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa

[ad_1]



Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar.

Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin.

Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa.

Cikin wadanda lamarin ya shafa kamar yadda jami’ar ta tabbatar akwai ɗalibai masu digirin farko da na gaba da shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *