Matatar Dangote Na Da Ƙarfin Samar Da Mai Fiye Da Buƙatar Nijeriya
[ad_1]
Matatar man fetur ta attajirin nan Aliko Dangote ta sake jaddada cewa tana da isasshen ƙarfin samar da fetur da sauran nau’o’in mai fiye da abin da ake buƙata a cikin gida a kowace rana. Matatar ta ce wannan mataki na taimakawa wajen tabbatar da wadatar mai a ƙasar tare da rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje.
A cewar sanarwar da matatar ta fitar, tana iya samar da lita miliyan 75 na fetur a kullum, yayin da ake amfani da kusan lita miliyan 50 ne kawai a fadin ƙasar. Haka kuma, tana samar da lita miliyan 25 na man dizal a rana, alhali buƙatar cikin gida na kusan lita miliyan 14 ce, da kuma lita miliyan 20 na man jiragen sama, wanda ya ninka adadin da ake bukata.
- Sojoji Sun Hallaka Babban Kwamandan Boko Haram, Abu Khalid, Da Wasu 10 A Borno
- Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Sake Jaddada Tabbatar Da Daidaitacciyar Kasuwa
Matatar ta bayyana cewa samun mai fiye da buƙata yana ba da damar tanadi da kuma daidaita kasuwa, musamman a lokutan da buƙata ke ƙaruwa ko kuma matsalolin sufuri suka taso. Ta ce wannan tsarin yana taimakawa wajen rage gaggawar shigo da mai da kuma ƙarfafa juriyar tsarin samar da mai a cikin gida.
Kamfanin ya ƙara da cewa masana harkar makamashi sun lura cewa samar da mai fiye da wanda ake amfani da shi yana taimakawa wajen ƙarfafa ajiyar tanadi da inganta daidaiton kasuwa, tare da ƙara ƙarfin tsarin rarraba kayayyakin man fetur a ƙasar.
Matatar Dangote ta kuma jaddada ƙudirinta na bin ƙa’idojin doka, tare da ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), domin tabbatar da cewa tsarin samar da man fetur da take bi ya dace da manufofin ƙasa na daidaiton kasuwa da bunƙasa tattalin arziki.
[ad_2]
Source link