Magidanci Ya Kashe Mutumin Da Yake Zargin Hulɗa Da Matarsa A Yobe

[ad_1]

Rundunar ƴansandan Jihar Yobe ta kama wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Hassan Umaru, bisa zargin kashe wani ɗan kauye mai shekaru 45, Sukari Abdul, sakamakon zargin cewa yana da alaƙa da matarsa.

A cewar kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ƙauyen Bundila, da ke Ƙaramar Hukumar Gulani ta jihar. Ya ce rikicin ya ɓarke ne a kasuwar ƙauyen, inda ake zargin Umaru ya kai wa Abdul hari da adda.

  • Yadda Mota Ta Kashe Mutane 3, Ta Jikkata 40 A Yobe
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe

An garzaya da wanda aka jikkata zuwa Cibiyar Lafiya ta Bularaba, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa. Rundunar ta ce an kama wanda ake zargi nan take, tare da kwato makamin da aka yi amfani da shi.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Emmanuel Ado, ya yi kira ga al’umma da kada su ɗauki doka a hannunsu, musamman a rikice-rikicen aure ko zamantakewa, yana mai jaddada muhimmancin kai ƙorafi ga hukumomin da suka dace.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *