Pedri ba zai buga wa Barcelona wasanni bakwai ba
[ad_1]
Ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona Pedri, zai yi jinyar makonni huɗu saboda raunin da ya samu a kofin Zakarun Nahiyyar Turai.
Dan wasan ya samu raunin ne a wasan da Barcelona ta doke Slavia Pra que da ci 4-2 a wasan mako na 7 a gasar.
A yau Juma’a, Barcelona ta sanar da cewa, Pedri zai yi jinyar makonni huɗu kafin ya koma taka mata leda.
Hakan na nufin Pedri ba zai buga wasan La Liga da Barcelona zata kece raini da Real Oviedo da Elche da Real Mallorca da Girona da kuma Levante ba.
Haka kuma ba zai buga wa Barcelona kofin Zakarun Nahiyyar Turai da za ta kara da Copenhagen ba, da kuma zagayen kwata fainal a Copa del Rey da Albacete ba.
Raunin Pedri babban koma baya ne ga Hansi Flick a ƙo ƙarin da yake na gannin Barcelona ta ci gaba da zama a saman teburin gasar La Liga, inda Real Madrid ke binta a mataki na biyar da tazarar maki 2 tsakaninsu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link