Hatsarin mota ya ci mutum 9 a Gombe — FRSC
[ad_1]
Matafiya 9 sun mutu a sakammakon wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Kaltungo–Cham, a ƙauyen Kaluwa da ke Ƙaramar Hukumar Kaltungo da ke Jihar Gombe.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) na jihar, Samson Kaura, ya ce hatsarin ya rutsa da mutane 18, inda biyar suka jikkata, huɗu kuma suka tsira ba tare da jin rauni ba.
Ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kaltungo domin samun kulawar likitoci, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiye gawa na asibitin.
Binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da matsalar birki.
“Da misalin ƙarfe 8:33 na safe ranar Litinin, wata tirela da ke gudu cikin sauri a kan hanya mai gangara ta buge wata mota Sharon daga baya, lamarin da ya sa motar ta yi juyi ta kife,” in ji Kaura.
Kwamandan ya jaddada cewa hukumar FRSC ta dade tana jan hankalin direbobi da su guji yin gudun da ya wuce kima, musamman a hanyoyi masu gangara da ke buƙatar kulawa ta musamman.
“Dole ne direbobi su riƙa tuka mota cikin natsuwa da gudun da za su iya sarrafawa, domin kauce wa asarar rayuka da dukiya,” ya ƙara da cewa.
Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su riƙa duba motocinsu kafin tafiya, musamman a wannan lokaci na bukukuwan ƙarshen shekara, domin gujewa aukuwar irin waɗannan haɗurra.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link