Kotu Ta Ɗage Sauraron Neman Beli Na El-Rufai Zuwa Gobe Laraba
[ad_1]
Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar Talata ta dage sauraron bukatar beli da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar zuwa ranar Laraba.
Dage sauraron ya biyo bayan zaman kotun da aka gudanar cikin tsauraran matakan tsaro, lamarin da ke nuna yadda jama’a ke son ganin yadda wannan shari’ar ta zargin cin hanci da rashawa za ta kare.
- Kwankwaso Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jos, Ya Nemi Hukumomi Su Ɗauki Mataki
- Majalisa Ta Buƙaci Sufeton ‘Yansanda Ya Binciki Kashe-kashen Rayuka a Filato
Lauyan tsohon gwamnan, Ukpong Akpan, ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan kammala zaman kotun, amma ya ƙi yin karin bayani.
Ya ce, “Ina bakin aiki, ba zan iya magana yanzu ba. Dole ne in je in shigar da martani. An dage sauraron bukatar belin zuwa gobe.”
Jim kaɗan bayan tashi daga kotu, jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (ICPC) suka raka El-Rufai daga harabar kotun zuwa cikin wata mota kirar Hilux fara.
Tun da farko, tsohon gwamnan ya koma kotu cikin tsauraran matakan tsaro domin ci gaba da sauraron bukatar belinsa.
[ad_2]
Source link