Yin Aiki Tare Don Fara Sabuwar Tafiya Ta Kirkire-kirkiren Kimiyya Da Fasaha A Yankin Beijing-Tianjin-Hebei

[ad_1]

Tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da aka yi a shekarar 2012, birnin Beijing ya himmatu sosai wajen karfafa aikin gina cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta duniya, tare da taka cikakkiyar rawa a matsayin tushen kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da karfafa yin hadin gwiwa da Tianjin da Hebei, da hada karfi da karfe, da kara kaimi ga ci gaba da inganta matsayin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a yankin Beijing-Tianjin-Hebei.

A yau, Zhongguancun na birnin Beijing, duk da ya kasance kasa da kashi 4 cikin dari na daukacin fadin birnin, ya ba da gudummawar kusan kashi daya bisa uku na alkaluman hada-hadar tattalin arziki (GDP) na birnin. Fiye da samfuran manyan manhajojin fasahar zamani na cikin gida 200 ne aka raya su a nan, wanda hakan ya kai kusan kashi 30 cikin dari na jimillar na kasa baki daya. Kazalika, a nan aka kyankyashe fiye da sabbin kamfanoni 90 masu zaman kansu dake da karfin jari, inda suka zama manyan ginshikai na habaka masana’antu.

Yayin da aka aiwatar da “shirin bunkasa ci gaban kasa da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14” daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata a hade alfanun da birnin Beijing ke da shi a fannin kimiyya da fasaha, da na Tianjin a fannin manyan masana’antu da bincike da samarwa domin tafiyar da wasu yankuna masu dacewa da ke Hebei, inda ake raya harkokin kimiyya da fasaha da kai masana’antu zuwa can daga Beijing da Tianjin. Shugaba Xi ya nuna hanyar da za a bi a aikace wajen ganin Beijing, Tianjin da Hebei sun yi hadin gwiwa domin gina wani katafaren muhalli na kirkire-kikiren kimiyya da fasaha.

A yau dai, Beijing, Tianjin da Hebei sun yi hadin gwiwa wajen daukar nauyin gudanar da muhimman ayyukan bincike sama da 220. Masana’antar kera motoci da aka sada ta da fasahar zamani ta samar da “da’irar samar da kayayyaki cikin sa’a daya tak”, tare da shigar da manyan kamfanoni sama da 300 a yankin Beijing-Tianjin-Hebei cikin tsarin ba tare da wata tangarda ba. A halin yanzu, adadin manyan rukunan kamfanoni na matakin kasa da ke yankin Beijing-Tianjin-Hebei ya karu zuwa bakwai, kuma tsarin hadin gwiwa na “bincike a birnin Beijing, da kerawa a Tianjin da Hebei” na samun kyakkyawan ci gaba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *