Kotu Ta Bayar Da Umarnin Ƙwace ₦1.1bn Na Wucin Gadi Da Aka Kwashe Daga Asusun Gwamnatin Kano

[ad_1]

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata, ta ba da umarnin kwace wasu kuɗaɗe na wucin gadi da suka haura Naira biliyan 1.1 da ake zargin an cire su ne daga Asusun Gwamnatin Tarayya na Jihar Kano a Bankin UBA, ba bisa ƙa’ida ba.

Mai Shari’a, Emeka Nwite ya bayar da umarnin ne bayan da Oluwafunke Bada, lauyan Hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC), ya gabatar da ƙarar akan zargin da aka yi.

  • Shugaba Xi Zai Gabatar Da Sakon Murnar Sabuwar Shekarar 2026
  • Trump Zaman Lafiya Yake Samar Wa Nijeriya Ba Yaƙi Ba – Riley Moore

Mai Shari’a Nwite, ya yanke hukuncin cewa, buƙatar ta dace kuma an amince da ita.

Mai Shari’ar ya kuma ba da umarnin a buga umarnin ƙwace kuɗin na wucin gadi a kowace irin jaridar ƙasa domin sanarwar ko akwai wanda yake ganin hukuncin bai cancanta ba, ko kuma kuɗin mallakinsa ne sai ya zo gaban kotu ya kare hukuncin.

Sannan Alkali Nwite ya ɗage shari’ar har zuwa ranar 21 ga Janairu, 2026 don bin ƙa’ida da jiran ko akwai wanda zai kare hukuncin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *