An kai hari shingen binciken ’yan sanda da kashe jami’ai 2
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ta tabbatar da cewa, wasu ’yan bindiga sun kai hari a shingen binciken ababan hawa da ke kan titin Agbani a daren ranar Alhamis, inda suka kashe ’yan sanda biyu tare da ƙona wata motar sintiri.
A cewar rundunar, an kai harin ne a ranar 15 ga watan Junairu, 2026, lokacin da ake zargin ’yan Ƙungiyar masu fafutukar kafa Ƙasar Biafra (IPOB) ne da kuma reshenta masu ɗauke da makamai, wato Eastern Security Network (ESN), suka buɗe wuta kan jami’an rundunar ’yan sandan da ke kula da matsalar ’yan sanda da ke shingen bincike.
“Ba zato ba tsammani maharan sun buɗe wuta kan tawagar ’yan sandan haka kawai, jami’an sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka tilasta wa maharan tserewa da raunuka daban-daban na harbin bindiga,” kamar yadda SP Daniel Ndukwe, kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana a wata sanarwa a ranar Juma’a.
A yayin musayar wutar, motar ’yan sandan ta ƙone ƙurmus, yayin da jami’an biyu suka samu munanan raunukan harbin bindiga. An garzaya da su asibiti domin samun kulawar gaggawa amma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsu.
Bayan afkuwar lamarin, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Enugu, CP Mamman Giwa, ya bayar da umarnin a tsaurara nemo waɗanda ake zargin, inda ya umurci jami’an tsaro da na sirri da su zaƙulo su tare da tabbatar da kama su.
“Kwamishinan ya umarci jami’an da su yi duk abin da ya dace tare da yin amfani da bayanan sirri don ci gaba da bin sawu tare da tabbatar da cewa an kama waɗanda suka tsere tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Ndukwe.
Rundunar ’yan sandan ta kuma tabbatar da ƙwato wata mota ƙirar Leɗus 330 SUƁ, da maharan suka ƙwace a baya daga hannun mai shi, suka yi amfani da su wajen kai harin. Motar ta samu hujewar harsashi da yawa daga harbin bindigar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link