ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya
[ad_1]
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu domin tsunduma yajin aiki muddin ta ci gaba da sakaci kan wasu buƙatu da take nema a biya.
A sanarwar gargaɗi da ASUUn ta fitar yau Litinin, ta ce daga jiya Lahadi, 28 ga watan Satumba, za ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 domin ta karkata akala kan buƙatun da take nema, ko kuma ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, inda daga nan zai rikiɗe zuwa na sai baba ta gani.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya sa wa hannu bayan taron majalisar zartarwar ASUU na ƙasa da aka gudanar a jami’ar Abuja a ranar Lahadi.
Ya ce ƙungiyar ta gaji da yadda Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da nuna halin ko in kula da harkar ilimi, musamman batutuwan da suka daɗe suna tattaunawa a kai
ASUU ta wassafa jerin buƙatunta da suka haɗa da bitar yarjejeniyar 2009 da samar da isassun kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i da biyan bashin albashin malamai da kuma samar da tsayayyen tsarin samun kuɗaɗen gudanarwa na jami’o’i.
“Ina sanar da cewa, idan bayan wa’adin kwana 14 gwamnatin tarayya ta kasa aiwatar da waɗannan buƙatu, ƙungiyar za ta fara da yajin gargaɗi na makonni biyu kafin ta shiga yajin aikin sai baba ta gani,” in ji sanarwar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link