Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Kanada Mark Carney

[ad_1]

Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Kanada Mark Carney wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, a babban zauren taron jama’a dake birnin Beijing.

Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce dole ne bangarorin Sin da Kanada su ci gaba da gina sabuwar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, bisa la’akari da tarihi da jama’a da kuma alhakin duniya, ta yadda dangantakarsu za ta kai wani yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa, don samar da mafi kyawun fa’ida ga al’ummomin kasashen biyu.

Shugaba Xi Jinping ya kuma ba da shawarwari guda hudu game da dangantakar Sin da Kanada. Na farko, ya kamata su zama abokan hadin gwiwa masu mutunta juna. Na biyu, ya kamata su zama abokan hadin gwiwa na neman ci gaba tare. Na uku, ya kamata su zama abokan hadin gwiwa da suka amince da juna. Na hudu, ya kamata su zama abokan hadin gwiwa masu taimakawa juna. Ya ce bangaren Sin yana son karfafa tuntuba da bangaren Kanada karkashin tsarin MDD da na kungiyar G20, da APEC, don shawo kan kalubalen duniya tare.

A nasa bangare, Mark Carney ya bayyana cewa, bangaren Kanada yana son gina sabuwar dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare mai karfi da dorewa tare da bangaren Sin. Kuma Kanada ta sake nanata niyyarta ta bin manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da mai da hankali kan fadadawa da karfafa hadin gwiwa da bangaren Sin a fannonin kasuwanci, makamashi, noma, kudi, ilimi, da sauyin yanayi. Haka kuma, bangaren Kanada yana son tuntubar mabanbamtan bangarori da dama tare da bangaren Sin, da kiyaye ra’ayin kasashe daban daban da ikon MDD, tare da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, la’akari da yanayin duniya mai sarkakiya.

Bayan ganawar, bangarorin biyu sun fitar da “Sanarwar hadin gwiwa ta ganawar shugabannin Sin da Kanada”.

Ganawar ta kuma samu halartar ministan harkokin wajen Sin Wang Yi. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *