Zulum ya raba wa magidanta 4,000 kuɗi da kayan abinci a Malam-Fatori
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fara rabon tallafin kuɗi da kayan abinci ga magidanta sama da 4,000 a garin Malam-Fatori da ke Ƙaramar Hukumar Abadam.
Tallafin ya shafi mutanen da aka dawo da su garuruwansu bayan shafe shekaru sama da 10 suna gudun hijira a Jamhuriyar Nijar sakamakon hare-haren ’yan ta’adda.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa kowane magidanci ya samu Naira 20,000, tare da buhun shinkafa da masara masu nauyin kilo 25, da kuma kayan sawa.
Haka kuma, mata sun samu Naira 20,000 da zannuwa domin rage musu wahalhalu.
Ya ce an bayar da tallafin ne saboda halin ƙunci da talauci da mutanen yankin ke ciki, tare da ƙarancin ayyukan yi.
A cewarsa, shirin zai taimaka wajen sake tsugunar da mutanen da suka dawo gida da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
“Wannan tallafi ba wai kuɗi da abinci kaɗai ba ne, yana nuna musu cewa gwamnati ba ta manta da su ba,” in ji Gwamna Zulum.
A yayin ziyarar, gwamnan ya duba gonakin noman rani da mutanen da suka dawo gida, inda ya ce noma shi ne ginshiƙin rayuwa.
Ya kuma yi alƙawarin samar da kayan aikin noma domin ƙara yawan amfanin gona da inganta wadatar abinci.
Gwamna Zulum ya ƙara da cewa sama da mutane 6,000 a Bosso, cikin Jamhuriyar Nijar, sun amfana da irin wannan tallafi, a matsayin godiya ga yadda mutanen Nijar suka kula da ’yan gudun hijirar Najeriya na tsawon shekaru.
Daga bisani, gwamnan ya yi rangadin dare a Malam-Fatori domin duba harkokin kasuwanci da wasu ayyukan more rayuwa.
Ya tabbatar wa ’yan kasuwa cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu ta hanyoyin samar da jari.
Haka kuma, ya bai wa Bataliyar Sojojin Najeriya ta 68 da ke Malam-Fatori motocin aiki da wasu kayayyaki domin ƙarfafa tsaro.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce gwamna Zulum ya nuna kulawa sosai ga mutanen da suka dawo daga hijira.
Ya gode wa gwamnan da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar bisa karamcin da suka nuna musu.
Sai dai ya roƙi gwamnati da ta ƙara tsaro a yankin domin gudun sake komawa gudun hijira, duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi.