Hisbah Ta Kama Mutane 9 Kan Yawon Dare A Kano
[ad_1]
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mutane tara; mata takwas da namiji ɗaya a wani samame da ta gudanar da daddare a jihar.
An kama su ne bisa zargin yawo ba gaira ba dalili da kuma neman kuɗi ta hanyar da ba ta dace ba.
- Wadanne Kasashe Ne Ba Su Taba Zuwa Kofin Afirka Ba?
- An Kama Mutanen Da Ake Zargin Barayin Babur Ne Dauke Da Makamai A Jihar Nasarawa
Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddeen Aminuddeen ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce an gudanar da samamen ne a wuraren da aka sani da yawaitar irin waɗannan ayyuka da daddare.
A cewarsa, an yi kamen ne a manyan tituna da unguwanni daban-daban na birnin Kano, ciki har da hanyar zuwa gidan gandun daji na Kano (Zoo), Banana a Zoo Road, Ahmadu Bello Way, Lamido Crescent, Tukur Road, Lodge Road da Sultan Road a Nassarawa GRA, hanyar zuwa Asibitin Nasarawa, titin Magajin Rumfa da Audu Bako Way.
Dakta Aminuddeen ya ce wasu daga cikin waɗannan wurare, kamar Ahmadu Bello Way da Lamido Crescent, wurare ne masu natsuwa da zaman lafiya a baya, amma yanzu sun fara zama wuraren da ake yawan yawo da daddare.
“Mun kama mata takwas da namiji ɗaya, abin takaici ma wasu daga cikinsu ƙananan yara ne,” in ji shi.
Ya yi kira ga iyaye da su ƙara sanya ido kan ’ya’yansu, musamman a wannan lokaci na bukukuwa.
Ya ƙara da cewa suma ci gaba da bincike, kuma za a ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka.
[ad_2]
Source link