Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikim wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin na daƙile laifuka da kuma kare jihar, musamman manyan hanyoyin shiga da fita na birnin Kano.
An bayyana cewa tashoshin mota na daga cikin wuraren da ake fuskantar barazanar tsaro saboda yawan zirga-zirgar mutane.
Rundunar ta musamman za ta mayar da hankali kan sanya ido, tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a tashoshin mota da sauran wurare a jihar.
Haka kuma za ta kula da wurare kamar gidajen mai da sauran wuraren da mutane ke taruwa.
Gwamna Abba, ya ce wannan mataki na nufin daƙile barazanar tsaro, inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma dawo tabbatar da kwanciyar hankali a jihar.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba mara wa hukumomin tsaro baya wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link