Hukumar Film ta kasa ta horar da marubuta 53 rubutun fim

[ad_1]



Hukumar Film ta kasa ta horar da marubuta 53 rubutun fim

Ranar Asabar 13-12-2025 aka gudanar da horo (training/workshop) ga marubuta 53 na masana’antar Kannywood wanda ta guda a karkashin Hukumar Fim ta Kasa wato Nigeria Film Corporation wadda Dakta Ali Nuhu yake jagoranta.

Horon ya gudana ne domin karara ƙwarewar wasu marubutan tare kyankyashe sababbin marubuta a masana’antar.

An gudanar da horon a dakin taro na Sarari Media and Telecommunications Hub da ke kan titin jami’ar Northwest Kano.
Ƙwararrun malamai masana rubutun fim daga tashar Arewa 24 kamar Nazir Adam Salih da Fauziyya D. Sulaiman da Zuwairiyyah Girei da Nasir NID su ne, suka bayar da wannan horo.
Yayin da Kabiru Anka da Nura Nasimat suka kasance masu kula da gudanar da horon.
Bayan kammala horon, an bayar da gwaji don tantance marubutan tare da ba su shaidar kammala dukar horo.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *