Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Makonni A UAE Da Turai
[ad_1]
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Nijeriya a ranar Asabar bayan halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week 2026 a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar Comprehensive Economic Partnership Agreement da UAE a yayin taron.
- Hukumar Kwastam Ta Fitar Da Wasu Sabbin Ƙa’idoji Ga Kamfanonin Rabar Da Kaya
- Shugaban Xi Ya Karbi Sabbin Jakadun Kasashen Waje A Kasar Sin
Yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa cinikayya da zuba jari, bunƙasa fasaha, da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin makamashi, noma, gine-gine da haƙar ma’adinai.
Shugaba Tinubu ya kuma sanar da cewa za a gudanar da taron haɗin gwiwa na Nigeria–UAE INVESTOPIA a Legas a watan Fabrairu domin jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.
Ya ƙara da cewa Nijeriya na shirin tara dala biliyan 30 a duk shekara domin ayyukan sauyin makamashi da kare muhalli.
Tun da farko a ranar Asabar, Onanuga ya wallafa wani bidiyo da ke nuna lokacin da Shugaba Tinubu ke barin otel ɗinsa a Abu Dhabi domin dawowa gida Nijeriya.
[ad_2]
Source link