Mahara sun kashe matan aure sun ƙona gidansu a Kano

[ad_1]



Wasu mahara sun yi wa wasu matan aure biyu kisan gilla a gidan mijinsu da keunguwar Tudun Yola a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Aminiya ta samu rahoton cewa maharan banka wa gidan wuta bayan da suka soka wa ɗaya daga cikin matan wuka har lahira, ɗayar kuma an tsinci gawarsa a cikin banɗaki.

Matan da aka yi wa wannan kisan gilla — Hauwa’u Yakubu da Zahra’u Aliyu — mata ne ga wani mai suna Alhaji Ashirin Shu’aibu Usaini.

Al’unnar unguwar Tudun Yola sun shiga tashin hankali da wannanan ɗanyen aiki.

Ɗan mai gidan, Anas Shu’aibu, ya yi zargin ana yi wa matan mahaifinsa wannan kisan gilla ne da tsakar rana lokacin da mai gidan da ’ya’yansa suka fita.

“Ba mu san abin da ke faruwa ba sai da daddare bayan mahaifinsmu ta kira cewa ina dawo gida, muna zuwa muka ga ɗaya yaqar a ƙone, ɗayar muka an kulle ta a banɗaki, ko da muka ɓalle ƙofar sai muka samu ita ma ta riga ta mutu.

“Da farko mun yi zargin gobara ce, amma sai muka lura cewa da alamar hari aka kai musu.”

Alhaji Shu’aibu, cikin kaɗuwa ya bayyana cewa “sun kashe Matana, sun ƙona gawar ɗayar. Ban san dalilin wannan rashin imani ba.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Koyawa ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa rundunar ta ta fara gudanar da bincike a kai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *