Mun kama ɗan ƙunar baƙin wake, mun ƙwato bindigogin AK-47 189 – Sojoji




Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar kama wanda ake zargin dan kunar bakin wake ne a jihar Borno tare da kama kayan da ake shirin amfani da su wajen kera bama-bamai na gida.

An kama wanda ake zargin mai suna Abubakar Mustapha a ranar Litinin ta hannun dakarun bataliya ta 152 tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, a garin Banki da ke Karamar Hukumar Bama a jihar.

Jami’in yada labarai na rundunar haɗin gwiwa da ke Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, ya ce an sami Mustapha da kayan da aka riga aka hada, wanda ke nuna shirin kai hari nan ba da jimawa ba.

“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin dan asalin Karamar Hukumar Bama ne, kuma an gano yana da wasu karin kayan da ke da alaka da ayyukan ta’addanci.

“Yanzu haka ana ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano masu daukarsa nauyinsa, abokan hulda da kuma yiwuwar dangantakarsa da kungiyoyin ta’addanci da ke aiki a yankin,” in ji Sani.

A wani labarin kuma dakarun da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru sun kama mota ƙirar Peugeot dauke da buhunan taki urea guda shida, wanda ake amfani da shi wajen kera bama-bamai na gida.

Binciken bayan haka ya kai ga kama dillalin takin da kwato wasu buhunan guda shida, wanda ya kai jimillar buhunan da aka kwato zuwa 12.

“An mika motar da takin nan take ga rundunar sojoji. Duk wadanda aka kama da kayan da aka kwato suna hannun dakarun tsaro domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakan shari’a,” in ji Sani.

A Arewa maso Yamma, rundunar sojin Najeriya ta kuma bayyana nasarori masu yawa a karkashin rundunar Operation Fasan Yamma.

Rundunar ta takwas ta sojojin ta ce dakarun sun kwato bindigogin AK-47 guda 189, dubban harsasai, da wasu kayan laifuka, tare da ceto mutane 1,023 da aka yi garkuwa da su a yayin hare-haren da aka gudanar a jihohin Sokoto, Katsina, Kebbi da Zamfara.

Yayin jawabi a taron 2025 haɗin gwiwa na yankin Yammacin Afirka da aka gudanar a hedikwatar rundunar, Kwamandan shiyya ta takwas ya ce ayyukan sun hallaka shugabannin ‘yan ta’adda da dama, sun rusa sansanonin ta’addanci, kuma sun rage yawan hare-hare a yankin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *