Kwastam ta kama fatar jakuna 718 a Bauchi

[ad_1]



Hukumar Kwastam ta Najeriya shiyyar Bauchi, ta ce ta kama fatar jakuna 718 da kudinsu ya haura Naira miliyan 24, da ake zargin ana kokarin fitar da su ƙetare ta haramtacciyar hanya.

Kwamandan Yanki na shiyyar, Abdullahi Kaila ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron manema labarai kan ayyukan yaki da safarar haramtattun kaya a hedikwatar rundunar da ke Bauchi.

Kaila ya ce, “Jimillar kudin harajin da aka biya na kayan da aka kama ya kai N24,313,217.00.”

Ya kara da cewa wannan kamun ya yi daidai da umarnin Shugaban hukumar ta Kwastam, Bashir Adewale, na aiwatar da tsauraran matakai kan safarar dabbobi da ke fuskantar barazanar karewa.

“Wannan aiki wani bangare ne na manyan ayyukanmu na yaki da safarar haramtattun dabbobi da kuma aiwatar da dokar gwamnatin tarayya kan hana fitar da fatar jakuna,” in ji shi.

Ya ce har yanzu kasuwanci da fitar da fatar jakuna haramun ne bisa dokokin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa, ciki har da wadda ta takaita kasuwancin dabbobin da ke fuskantar barazanar karewa.

A cewarsa, an kama mutane biyu, ciki har da direban motar da ta ɗauko kayan da kuma mai kayan, kuma za a gurfanar da su bisa dokar hukumar ta 2023 da sauran dokokin kare muhalli.

Kaila ya kara da cewa nasarar wannan aiki ta samu ne sakamakon ingantaccen hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, wanda ya inganta musayar bayanan sirri tare da tarwatsa hanyoyin masu safara a yankin.

“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Duk wanda aka samu da hannu a safarar haramtattun kayayyakin dabbobi za a kama shi, a gurfanar da shi, kuma a hukunta shi bisa doka,” in ji Kaila.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *