Yajin aiki: Likitoci sun ba wa gwamnati wa’adin kwana 30
[ad_1]
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 30 domin biyan buƙatun ’ya’yanta, ko kuma ta fuskanci yajin aiki.
Wa’adin na ƙunshe ne a sanarwar Bayan taron ƙungiyar, ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dakta Mohammad Suleiman; Sakatare Janar, Dakta Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Yaɗa Labarai, Dakta Abdulmajid Ibrahim.
Shugaban NARD, Dakta Suleiman, wanda aka zaɓa a taron domin maye gurbin Dakta Tope Osundara, ya ce wannan wa’adin ba a bayar da shi da wasa ba.
“Ba za mu ci gaba da kallo mambobinmu suna aiki cikin yanayi marar tsaro yayin da aka yi watsi da walwalarsu ba. Idan ba a warware matsalolin cikin kwanaki 30 ba, za mu ɗauki mataki,” in ji shi.
Muhimman bukatun sun haɗa da biyan bashin kuɗin karin girma da ya taru, sakin sabbin lissafin alawus na ma’aikata, dawo da likitoci biyar da aka kora daga Asibitin Koyarwa na Tarayya a Lokoja, da kuma ɗaukar mataki kan jinkirin da aka yi wajen sabunta tsarin albashin likitoci (CONMESS).
Sanarwar bayan babban taron ƙungiyar da ya gudana a Katsina ya kara da cewa, “Babban taron ya buƙaci cewa Gwamnatin Tarayya ta biya duk kuɗaɗen karin girma da ake binsu a cikin kwanaki 30.
“Haka kuma, Ma’aikatar Lafiya da Asibitin Koyarwa na Tarayya, Lokoja, su dawo da likitoci biyar da aka kora a cikin kwanaki 30.”
Ƙungiyar ta kuma koka kan tsawon awannin aiki da ta bayyana a matsayin barazana ga lafiyar ma’aikata, inda ta umarci mambobinta kada su yi aiki fiye da sa’o’i 24 a jere daga ranar 1 ga Oktoba.
Ta buƙaci Ma’aikatar Lafiya ta tsara jadawalin aiki da ya yi daidai da tsarin ƙasashen duniya.
NARD ta kuma nuna damuwa kan matsalar barin Najeriya da likitoci ke yi da ɗaukar ma’aikata kan kwangila sa matsalar asibitoci da kuma ware likitoci masu koyon aiki daga tsarin ma’aikatan gwamnati.
Ta roƙi gwamnati ta aiwatar da tsarin maye gurbin duk ma’aikaci da ya bar aiki domin rage ƙarancin ma’aikata a asibitoci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link