Hotunan wuraren da Amurka ta kai wa hari a Sokoto
[ad_1]
Al’ummar garin Tangaza da Tambuwal a Jihar Sakkwato sun shiga cikin firgici a ranar Alhamis yayin da Amurka ta ƙaddamar da farmakin soji kan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Shugaba Donald Trump ya sanar da matakin na soja a wani saƙon da ya wallafa a shafin sada zumunta da yammacin ranar Alhamis.
Mazauna Ƙananan hukumomin Tangaza da Tambuwal a Jihar Sokoto, sun tabbatar da hare-haren da jiragen yaƙi marasa matuƙa suka kai wa unguwanninsu, da sojojin Amurka suka kai.
Binciken da wakilinmu ya samu ya nuna cewa, ɗaya daga cikin hare-haren ya afku ne a gundumar Jabo da ke Ƙaramar hukumar Tambuwal, unguwar da a baya ta fuskancin rashin tsaro.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce hare-haren da aka kai ta sama wani ɓangare ne na ayyukan haɗin gwiwa da ake yi tsakanin Najeriya da Amurka.
Ga hotunan wuraren:







Masu alaƙa
[ad_2]
Source link