Hatsarin Mota Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 5, Ya Jikkata 13 A Filato

[ad_1]

Aƙalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 13 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a shataletalen Zangzat a garin Langtang, cikin ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa a Jihar Filato, a ranar Lahadi da safe.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 3 na asuba, ya shafi wata babbar mota (traila) da ke ɗauke da ƴan kasuwa daga Shendam zuwa Jos, ta hanyar Langtang. Motar ta kife ne a kusa da shataletalen Zangzat, lamarin da ya janyo asarfrrxaar rayuka da jikkata mutane da dama.

  • Gwamnan Filato Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Ƙungiyar Da Ke Safarar Makamai Tare Da Kama Mutane 3 A Filato

Shugaban ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa, Hon. Pirfa Jingfa Tyem, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan aukuwar hatsarin a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Kum Precious Yakubu, ta sanya wa hannu. Sanarwar ta ce rahotannin farko sun nuna cewa hatsarin ya shafi mota mai rijistar Jihar Filato mai lambar JJN 383 YZ.

A cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa gudun wuce gona da iri da kuma lodin fiye da ƙima ne suka haddasa hatsarin. Sanarwar ta kara da cewa mutane biyar sun mutu nan take, yayin da kusan mutane 13 suka samu raunuka mabambanta, kuma tuni aka garzaya da su Babban Asibitin Langtang domin samun kulawa.

Hon. Tyem ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa. Ya kuma buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) da ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a kuma aiwatar da dokokin hanya, musamman a kasuwanni, tashoshin mota da manyan hanyoyi, yayin da ya gargaɗi direbobi da masu dakon kaya da su guji gudu da lodin fiye da ƙima domin kare rayuka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *