Dalilin Manoma Na Rungumar Irin Farin Wake A Jihar Benuwe
[ad_1]
Daga Abubakar Abba
Bayan kammala girbin kakar noman bana, wasu daga cikin manoman Farin Wake a Jihar Benuwe, sun bayyana gamsuwarsu, kan rungumar shirin fara yin noman Waken da wani sabon Irinsa da aka samar.
Sun sanar da hakan ne, musamman kan girma da nau’in da Irin Waken yake da shi da kuma dandanon da Waken yake da shi.
- Gwamnan Gombe Ya Kafa Hukumar Kula Da Wutar Lantarki
- NSCDC Ta Kama Mutane 3 Kan Kisan Jami’inta A Kano
Daya daga cikin manoman, mai suna Yusuf Dindah, ya bayyana cewa; nau’i da kuma girman na sabon Irin Waken, hakan ya yanke shawarar shi zai shuka a kakar noma ta badi.
A cewarsa, tuni ya fara tsara guraren da zai shuka sabon Irin na Waken a cikin gonarsa.
Ita ma wata manomiyar Farin Waken mai suna Akepra Nadoo, wadda take kanana da kuma manyan Farin Wake ta sanar da cewa; Waken na da saurin dahuwa a wajen yin girki.
A cewarta, shekaru da dama da suka gabata, sun gano cewa; a wajen yin girki, sabon Waken na da saurin dahuwa, kuma yana da dandado, sannan kuma zan zabe shi domin noma shi a kakar noma ta badi.
Kazalika, kamar dai a bangaren Nadoo da Dindah, wadanda su ma manoman Farin Waken ne, sun bayyana jin dadinsu bisa samar da sabon Irin na Farin Wake da cibiyar bunkasa aikin noma ta kasa da kasa, wato IITA tare da hadaka da jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke garin Makurdi suka yi.
An dai gabatar da wannan sabon Irin na Farin Waken ne, a wani bajekolinsa da aka gudanar a jami’ar, wanda kuma ya kasance yana jurewa kowanne irin yanayi na yin noma.
Bugu da kari, sabon Irin na Farin Waken zai iya kara bunkasa samar da wadataccen Waken da kuma kara samar da kudaden shiga ga manoman da za su shuka shi.
A lokain bajekolin na Irin Farin Waken manoman Farin Wake da dama, sun duba yadda sabon Irin na Farn Waken yake tare da kuma yaba wa kwararun da suka samar da shi.
Manoman Farin Wake kamar irin su, Praise Asen da Ikyaahemba John da kuma Elizabeth Edward, sun jinjana bisa samar da wannan sabon ci gaban.
Sun bayyana cewa, sun zabi wannan sabon Irin na Farin Waken wadanda suka kasance manya masu ruwan kasa da kuma kananan Irin na Farin Waken, domin a baya sun taba shuka su tare da yin amfani da shi, wadanda kuma suna da dandano.
Sai dai, Nguemen Iorshi ta fi sha’awar ta zabi kananan Irin Waken, wanda ta sanar da cewa, shekaru hudu da suka wuce, ta shuka shi a gonarta, kuma ta samu albarka mai yawan gaske.
A jawabinsa a wajen taron bajekolin, wani mai renon sabon Irin na Farin Waken, Godspower Ekeruo, da ke jami’ar ta Joseph Sarwuan Tarka ya bayyana cewa; akwai wani shirin da ke tafe na samar da wasu sabbin Irin na Farin Waken.
Ya sanar da cewa, an yi wannan bajinkolin na sabon Irin Farin Waken a jami’ar ne, domin manomansa su zabi sabon Irin da suke da bukata.
“Wannan sabon Irin na jure wa duk wani nau’i na cututtukan da ke harbin Farin Wake, kuma bisa zabin da manomansa suka yi, hakan zai sanya mu kara tunanin samar da wasu sabbin Irin na Farin Waken,” in ji shi.
“Muna ci gaba da kasancewa a nan ne, saboda amfanin manoman na Farin Waken, musamman domin su dubi kan sabon Irin da kuma wanda suke son su zaba,” a cewarsa.
Shi kuwa, wani kwararre a fannin aikin noma da ke jami’ar ta Joseph Sarwuan Tarka, Dakta Teryima Iorlarmen, ya shawarci manoman na Farin Wake da su yi amfani da wannan sabon Irin na Waken, musamman domin kara bunkasa sana’ar tasu ta noma.
“Mu a wannan jami’ar, mun kara inganta wannan sabon Irin Farin Waken, wanda a shekarun baya ba a shuka shi a a Jihar Benuwe,” in ji shi.
Ya kara da cewa, amma a yau Jihar Benuwe ta samarwa da kasar nan wannan sabon Irin na Farin Waken mai inganci, wanda kuma Jihar Neja ke bi mata baya.
“Mun kirkiro da samfurin sabon Irin na Farin Waken kamar na FUAMPEA 1, 2, 3, 4, 5, wanda a shekaru goma da suka gabata, zai yi matukar wuya a noma shi a jihar ta Benuwe, in ji Dakta Teryima.
“Ba wai za mu tsaya kan kirkiro da nau’in na FUAMPEA 5, za mu kara zagewa, musamman domin shiga gaban jami’ar Ahmadu Bello, domin mu kara kirikiro da wani sabon nau’i na FUAMPEA 20+ ,” a cewarsa.
[ad_2]
Source link