Wata mata ta haifi ’ya’ya huɗu a Bauchi
[ad_1]
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata, kuma tana ci gaba da jinya tare da ’yan huɗun.
A washegarin haihuwar, Hajiya Halima Garba, matar shugaban asibitin (CMD), ta ziyarci mai jegon tare da mijinta da manyan ma’aikatan asibitin.
Ta taya iyalan murna tare da addu’ar samun lafiya cikin gaggawa.
Kamar yadda ta saba a duk lokacin da aka samu irin wannan lamari, Hajiya Halima ta bayar da tallafin kuɗi, kayayyakin jinya da kayan jarirai domin taimaka wa iyalin. Ta kuma bai wa wasu majinyata tallafin kuɗi.
Shi Dakta Dauda Abubakar Katagum, ya taya iyalan murna, inda ya bayyana haifuwar jariran huɗu a matsayin baiwa da kyauta daga Allah.
Angon ƙarni, Buba Adamu, wani manomi daga ƙauyen Gambaki a ƙaramar hukumar Katagum, ya bayyana farin cikinsa tare da godiya bisa karamcin da aka yi musu.
A matsayin nuna godiya, ya sanya wa ɗaya daga cikin jariran mata suna Halimatu Sa’adiyya, wato takwara ga uwargidan CMD.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link