Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato
[ad_1]
Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar mota ta yanke sakamakon ambaliya.
Yayin da yake tafiya, jirgin ya bugi wata ƙaramar gada ta nutse a ruwa, lamarin da ya jawo mutuwar mutum tara, yayin da wasu suka samu rauni.
Rahotanni sun ce ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba saboda ya ɗauki mutane fiye da kima.
Har yanzu hukumomin agajin gaggawa ba su fitar da wata sanarwa ba kan hatsarin.
A nasa martanin, Sanata Ibrahim Lamiɗo, Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga al’ummar yankin tare da kiran gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro da gyaran hanya tsakanin Sabon Birni da Goronyo.
Ya ce rashin tsaro da matsalar tituna na jefa mutanen yankin cikin hatsari, tare da jaddada cewa gwamnati na da alhakin kare rayukan jama’a da kuma inganta rayuwarsu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link