Yadda Janar Murtala ya sauya Najeriya cikin kwanaki 200

[ad_1]



Da safiyar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 1976, ƙarar harbe-harbe suka karaɗe babban birnin Najeriya na wancan lokacin wato Legas. Shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammed, aka yi wa kwanton-ɓauna sannan aka kashe shi a wani juyin mulkin da bai yi nasara ba.

An kashe shi yana da shekaru 37 kacal, kuma bai wuce kwanaki 200 a kan mulki ba. Amma duk da wannan gajeren lokacin, ya bar tarihi mai ɗorewa da har bayan fiye da rabin ƙarni, sunansa yana ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya da ma Afirka.

Shekaru 50 bayan rasuwarsa, an sanya sunan Murtala Muhammed a manyan gine-gine a Najeriya; filin jirgin sama mafi girma a Legas, makarantu, tituna da asibitoci.

A kowacce shekara, gidauniyar Murtala Muhammed, ƙarƙashin jagorancin matarsa Ajoke Muhammed, tana shirya taruka domin tunawa da shi. Kabarinsa a Kano ya zama wurin ziyara, inda ake yi masa addu’o’i na musamman a kowacce Juma’a.

Ga yawancin ’yan Najeriya, mulkinsa na ɗan gajeren lokaci ya zama wani mizani na gaskiya da kishin ƙasa.

Wane ne Murtala?

An haife shi a unguwar Kurawa da ke Kano, ranar 8 ga watan Nuwamba, 1938. Ya yi karatu a Kwalejin Barewa, sannan ya halarci makarantar sojoji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst a Ingila.

Ya fafata a yaƙin rikicin ƙasar Kwango, sannan ya taka rawa a Yaƙin Basasar Najeriya. Saboda jarumtarsa, aka yi masa laƙabi da “Jangwarzo.”

Bayan ya karɓi mulki daga Janar Yakubu Gowon a watan Yulin 1975, ya fara kawo sauye-sauye a nan take. Ya kori dubban ma’aikatan gwamnati da aka zarga da aikata rashawa, ya ƙaddamar da yaƙi da rashin ɗa’a, ya goyi bayan samun ’yancin Afirka, kuma ya fara aikin sauya babban birnin Najeriya daga Legas zuwa Abuja.

Kisan da aka yi masa ya katse wannan shirin sauya tsarin da har yanzu ake ganin babu wanda ya kai shi.

Jihohin da ya ƙirƙira

A ranar 3 ga watan Fabrairun 1976, Murtala ya ƙirƙiri sabbin jihohi guda bakwai: Bauchi, Binuwai, Borno, Imo, Neja, Ogun da Ondo. Hakan ya ƙara yawan jihohin Najeriya daga 12 zuwa 19. Wannan mataki ya kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake ci gaba da tuna mulkinsa na gajeren lokaci.

La’akari da jarumtarsa da kishin ƙasa, ya sa Murtala ya zama tsohon shugaban mulkin soja ɗaya tilo da aka sanya hoton shi a jikin kuɓin ƙasar, wato Naira 20.

Yadda ya sauya Najeriya cikin kwanaki 200 – Masanin tarihi

Masanin tarihi kuma mai bincike mai zaman kansa a Kano, Dr Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana sauye-sauyen da Murtala ya kawo a Najeriya cikin ’yan watannin da ya yi a kan mulki.

Wasu ‘yan uwa da abokan arzikin Murtala suna masa addu’a gefen kabarinsa

Ya ce duk da gajeren lokaci, tsohon Shugaban ya ƙirƙiri jihohi bakwai, ya fara Shirin sauya babban birnin ƙasar daga Legas zuwa Abuja, sannan ya kafa kundin tsarin mulki na 1979 wanda har yanzu ake amfani da shi, kuma ya jagoranci sauya manufofin Najeriya na ƙasashen waje kan Afirka.

Ya ƙara da cewa manufofin sun zama sanadiyyar samun ’yancin kan ƙasar Namibiya da Afirka ta Kudu, wanda ya hanzarta rushe tsarin mulkin wariyar launin fata.

Sai dai masanin ya nuna takaicin cewa shugabannin yanzu sun kasa ginawa kan waɗannan nasarorin.

“Murtala ya yi yaƙi da rashawa kuma ya tsaya kan kyakkyawan shugabanci. Waɗannan abubuwa ne suka sa har yanzu muke kewarsa,” in ji Dr Kurawa.

Asalin duk mahaifansa ’yan Kano ne, ba ɗan Edo a ciki – Ƙanwarsa

Ƙanwar Murtala, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ta yi ƙoƙari wajen gyara abin da ta kira da kuskuren fahimtar da aka daɗe ana yaɗawa game da asalinsa.

Kanwar Murtala, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu

Ta ce, “Akwai maganganu da yawa da kuskure ne game da asalinsa, cewa daga Edo ne. Wannan ba gaskiya ba ne. Murtala ɗan Kano ne, daga dangin sarautar da malamai a Kano. Na bi salsalar dukkan kakanninsa kuma na fitar da sahihan bayanai a kai.”

Ta jaddada cewa ɗan uwanta Bahaushen Kano ne.

Ta tuna da shi a matsayin mutum mai son bin ƙa’ida da gaskiya, wanda halayensa suka zama fitilar yadda ya mulki Najeriya.

“Bai taɓa yarda da sakaci ko wasa da amana ko son zuciya ba. Waɗannan halayen ne suka shafi yadda ya mulki Najeriya, saboda yana da gaskiya, kishin ƙasa, kuma ya yi duk abin da zai iya don ganin Najeriya ta wanzu. Wannan ma shi ne ya jawo har aka kasha shi,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa tana da shekaru 18 lokacin da aka kashe shi, kuma har yanzu tana tuna ziyararsa lokacin da mahaifinta ya rasu.

Balaraba ta ce bayan kisan, ’yan Najeriya da dama sun yi rika girmama shi, ta hanyar sanya wa ’ya’yansu sunansa ko sunan mahaifiyarsu, Ramat a matsayin girmamawa.

Mahaifina ya rayu a kan gaskiya – Risqua Murtala Muhammed

Ɗan marigayin, Risƙua Murtala Muhammed, ya ce shekara 50 ba tare da mahaifin nasa ba lokaci ne na tunawa da abubuwan alherin da ya yi.

Dan Murtala, Risqua Murtala Muhammad

Ya ce, “Lokaci ne na godiya ga abubuwan da Janar Murtala Ramat Muhammed ya bari. Bayan shekaru 50, har yanzu ana tuna shi saboda abubuwan alherin da ya yi. Ya tsaya kan yaƙi da rashawa, gaskiya, adalci, da daidaito. Zai yi wahala kuma ƙasa ta ci gaba ba tare da waɗannan abubuwan ba.”

Ya kuma ce, “Ba kawai a Najeriya ba, har ma a Afirka, ya yi yaƙi don ’yantar da ’yan’uwanmu a Angola, Namibiya da Afirka ta Kudu.”

Ya mutu ba tare da ya bar ko sisi ba – Ambasada Aminu Wali

Tsohon Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Ambasada Aminu Wali, wanda ɗan uwan Murtalan ne, ya ba da labarin abin da ya sani a kan marigayin.

Kabarin Murtala da ke kusa da masallacinsa a Kano

Ya ce, “Marigayi Murtala yana da halaye na gari. Ya kasance mai gaskiya, mai adalci a duk abin da ya yi, kuma mai damuwa da walwalar mutane.

“Ya mutu ba tare da dukiya ba. Sau da dama idan na je gidansa a Legas, zai nuna min lalitarsa babu kuɗi, yana cewa, ‘Idan ba ka biya wa ’ya’yanka (’ya’yan cikinsa) kuɓin makaranta ba, za a kore su.’ Wannan shi ne Murtala.”

Ya kuma tuna kasancewarsa a cikin jirgin da ya ɗauko gawar Murtala daga Legas zuwa Kano har zuwa binne shi.

Wali ya kuma ce, “Bayan shekaru 50, babu wani shugaba da ya Mulki Najeriya da zan iya kwatanta shi da Murtala dangane da jajircewa da kishin ƙasa.”

Kullum sai mun yi masa addu’a a nan – Limamanin masallacin Murtala

Babban Limamin Masallacin Murtala Muhammed da Hausawa, Kano, Imam Kabiru Badamasi ɗantaura, ya ce marigayi Murtala mutum ne mai addini sosai.

Masallacin Murtala Muhammed da ke Hausawa, Kano

Ya ce: “Kowa ya san Murtala mutum ne mai gaskiya, kishin ƙasa da addini. Har ma saboda addininsa aka kashe shi a hanyarsa ta zuwa masallaci.”

Ya bayyana cewa bayan kowace sallar Juma’a, suna yi masa addu’a ta musamman.

Ya ƙara da cewa: “A kowace Fabrairu, ana yi masa addu’a ta musamman domin tunawa da watan da aka kashe shi. Mutane da dama suna zuwa kabarinsa daga wurare daban-daban su yi masa addu’a. A bana musamman saboda cikar sa shekaru 50, an yi masa addu’a ta musamman a Juma’ar da ta gabata.”

Imam Dantaura ya kuma bayyana hikimar gina masallaci da makarantar Islamiyya kusa da kabarinsa.

Ya ce, “An yi haka ne domin ya sami albarka da addu’o’in masu zuwa ibada. A kowace Juma’a, a kowanne want azumin Ramadan, ana yi masa addu’a.

“A kowanne watan Fabrairu (watan da aka kashe shi) ma idan ya zagayo, ana yi masa addu’a ta musamman a nan. Duk wanda ya san ikon shugaban ƙasa, ya zo ya ga kabarinsa, hakan darasi ne ga kowa,” in ji limamin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *