AFCON 2025: Nijeriya Ta Kai Zagayen ‘Yan 16 Bayan Doke Tunisia
[ad_1]
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya da ke buga gasar kofin ƙasashen nahiyar Afirika yanzu haka a ƙasar Morocco ta samu nasarar kai wa matakin zagayen ‘yan 16 bayan ta doke ƙasar Tunisia a wasa na biyu da ta buga a rukunin C na gasar.
Nijeriya ta zama ƙasa ta biyu bayan Masar da ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin zagayen 16 a gasar.
- Majalisar Dokokin Kasar Sin Ta Kammala Zaman Zaunannen Kwamitinta
- AFCON 2026: DR Congo To Yi Wa Senegal Fankale
Super Eagles ta haɗa maki 6 da ƙwallaye biyu a wasanni biyu da ta buga, yayin da aka jefa mata ƙwallaye uku a wasa biyu.
Victor Osimhen ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Tunisia tun kafin zuwa hutun rabin lokaci, bayan an dawo ne kyaftin ɗin Nijeriya Wilfried Ndidi ya jefa ƙwallon ta biyu a minti na 51 kafin Ademola Lookman ya jefa a minti na 67.
Wasan na yau ya kasance mai matuƙar armashi duba da cewa dukkanin ƙasashen biyu ba kanwar lasa ba ne a fagen taka leda a Afirika.
[ad_2]
Source link