An Samu Manyan Nasarori A Kannywood A ‘Yan Shekarun Nan –Maryan CTB
[ad_1]
Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana, daga cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood. Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wata fitacciyar jarumar wacce ta shafe sama da shekaru ashirin a cikin masana’antar Kannywood wato, HAJ MARYAM SULAIMAN wacce aka fi sani da MARYAM CTB. Inda ta bayyana wa masu karatu babban ci gaban da masa’antar Kannywood ta samu a yanzu, da kuma wasu abubuwa da masana’antar ta rasa a yanzu sabanin shekarun baya. Baya ga haka jarumar ta yi kira ga furodusas kan wani nauyi da ya kamata su sauke shi, hadi da wasu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi masana’antar da kuma masu yunkurin shiga cikin masana’antar, har ma da wasu batutuwan masu yawa.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
- An Yi Matukar Inganta Harkokin Sadarwa A Kasar Sin Cikin Shekaru Biyar Da Suka Wuce
- Da Sahalewar Nijeriya Bayan Samun Bayanan Sirri Amurka Ta Kai Hari — Tuggar
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Sunana Haj. Maryam Sulaiman, wacce aka fi sani da Maryam CTB.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni dai an haife ni a Gumel a Jihar Jigawa, Lokacin ina shekara daya kakata ta dauko ni, na girma a Fagge. A saka ni a ‘Fagge Prinary School’, na je ‘GGC Dala’ ban gama ba kakata ta cire ni ta yi min aure.
Wane rawa ki ke takawa a cikin masana’antar Kannywood?
Ina taka rawar Uwa ta kirki ko uwar da ba ta da kirki, yawanci dai shi ne rawar da nake takawa a Kannywood.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?
Ni daman na fara da gidan TB ne na CTB tun kafin ma a san za a bude Kannywood. Lokacin da aka yi min aure na farkon bayan na fito sai na koma makaranta, na koma ‘Women Centre’ ta kofar Nassarawa. To, ina ‘Women centre’ kuma sai nake zuwa CTB, ni ‘Artist’ dinsu ce, ina zuwa ina yi masu shirye-shirye a gidan talabijin na CTB. Kamar shirin; Dan Iyalanku da kuma wani shiri ‘Ku Matso Yara’. Daga nan ne sai CTB ta kirkiri wata drama wacce take kamar ‘series’, ana ce mata ‘Kowa ya bar gida’. To, wannan ‘Kowa ya bar Gida’ shi ne farkon yin drama ta a rayuwa. Ina cikin wannan shiri aka gayyace ni zuwa wannan shiri, kuma ni da Kabiru Maikaba da Marigayiya Hauwa Ali Dodo, duk su ma fim dinsu na farko kenan.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Gaskiya shekarun da dan yawa, idan aka cire na CTB, fara fim dina a Kannywood zai kai shekara ashirin da wani abu, tunda fim din da na fara da shi fim din Dan’Azumi Baba ne wato Kamaye, wato Babban Gari, shi ne fim din da na fara yi.
Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance?
Gwagwarmaya ai kuwa akwaita, domin kuwa duk wanda yake harkar jama’a dole yana cikin gwagwarmaya. Wani gwagwarmayar da dadi wani kuma babu dadi. Kowace al’umma akwai irin kallon da take yi mana, wasu suna yi mana kallon mutane ne wadanda suke fadakarwa, kuma mutane ne wadanda suka dauki fim sana’a, kuma sun tsaya a kansa, wasu kuma suna yi mana kallon sabanin haka. Dan wasu suna kallon mu mutane ne da ba mu da tarbiyya, kuma ba ma bawa al’umma tarbiyya, wanda kuma labarin ba haka yake ba. Mu mutane ne masu tarbiyya daga gidan tarbiyya muke, duk wanda ya zo fim ya lalace to, daman da abin sa ya zo, ba fim bane ya saka shi.
Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Kamar yadda na fada miki cewa ni ba da Kannywood na fara ba, kafin ma a san Kannywood da CTB na fara. Alhamdulillah Mahaifina da Mahaifiyata masu fahimta, lokacin suna raye. Bayan da na bar CTB zan yi fim, na kai masu fom na ce, ga shi zan yi fim, ku sa min hannu. Iyayena suka saka min albarka, nasihar mahaifina shi ne; na rike mutunci na, kuma na rike girmana, kuma kar na sake na yi abin da zai janyo wa gidansu abin kunya ko abin da zai bata musu suna,, tunda babban gida ne gidan masarautar Gumel ne, ni dai sai sam barka, an saka min albarka.
Ya karbuwar fim dinki na farko ya kasance ga masu kallo?
Kowa ya san a wancan lokacin Babban Gari daga 1 har 2 har 3 ya karbu, karbuwa sosai ma kuwa. Saboda haka gaskiya ni ban samu wani kalubale ba, tunda na fara fim cewar ko wani fim da nayi bai karbu ba ko kuma ban ji dadinsa ba, gaskiya babu.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Ba zan iya tuna adadin finafinan da nayi ba, sabida suna da yawa, sai dai na kiyasta. Ina jin za su fi dari biyu ko dari uku, tunda shekarun da yawa an yi ayyuka.
A finafinan da ki ka fito ciki, wanne ne ya zamo bakandamiyyar ki?
Kowanne fim da nayi bakandamiyata ne gaskiya, babu wani fim da zan ce wai yau ga shi tunda suna da yawa, idan na zabi wani ma ba mamaki masu karatu su ba shi suke so ba. Na yi finafinai da dama wanda har yanzu suna kan tashensu kamar akwai; Kishiyata, Manyan Mata, Garwashi, na baya baya kenan.
Wadanne irin nasarori ki ka samu game da fim?
Na samu nasarori masu yawa wanda ba zan iya lissafa su ba, ba ma a Nigeria ba, a sauran kasashen duniya da nake zuwa kamar su; Ghana, Chad, Cameroon, Niger. Irin karbuwar da nake samu da irin alfarmar da nake samu da kuma masoyan da nake samu ai babbar nasara ce.
Ko akwai wani fim wanda ki ka fito cikinsa, daga baya ki ka yi da-kin-sanin fitowa cikinsa?
Sunan fim din Uwata Ce,, labari ne da aka yi shi a gaske. Babbar mace ce da ‘ya’yanta manya, sai ta rike dan kishiyarta ya girma a hannunta, kishiyar kuma ta rasu. Tana da wata kawa me budurwar zuciya, kawar tana neman yara kanana, karshe ta ziga kawar ta ta da ita ma ta fara neman kananan yara tunda ita ma matar da take rike da dan, mijinta ya rasu daga ita sai yaranta da dan kishiyarta. Ita da ta tashi hauka sai ta nemi dan kishiyar har ya yi mata ciki. To, wannan babban kalubale ne, saboda wannan fim din na sha kiraye-kirayen malamai ma suna yi min nasiha, me ya sa ban taba fitowa a fim ba mutunci irin wannan ba. Na kan ce musu su yi hakuri, duk wanda ku ka ga ya fito a fim ya yi rashin mutunci ba wai ainihin halinsa bane na zahiri, a’a! dora masa aka yi. Kuma a Hizbah aka kawo labarin ‘yan’uwan wanda abun ya faru da su, su ne suka kawo labarin suka ce a yi fim da shi. Muna so mu fadakar ne, mu wayar da hankalin mutane.
Wane fim ne ya taba faranta miki rai, kuma me ya sa?
Wani fim ne abin da ya farantan rai, garin muka bari muka je muka yi aiki cikin farinciki, cikin girmamawa, cikin mutuntawa, cikin kulawa. Kuma ikon Allah fim din yayi nasara, kuma na samu alkhairi sosai dalilin fim din.
Ko kina da ubangida a cikin masana’antar Kannywood?
Ba ni da ubangida a harkar fim, sai dai abokanan mutunci wadanda na dauke su kamar iyaye, ko ‘yan’uwa, ko ‘ya’yana. Amma wani ubangida takaimaimai wanda zai fito ya tsaya min ko dalilinsa na shiga babu. To, ban ki ba akwai Baba Isah Jaa, tunda CTB ma gabadaya kafin na shige ta Allah ne sanadi, Baba Isah Jaa shi ne. Lokacin ba zan manta ba suna wani fim Bakan Gizo, lokacin Allah ya hada ni da shi, kuma shi ya fara kai ni CTB. Idan ma da wani ubangida bai wuce shi ba.
Ya ki ka dauki fim a wajenki?
Kamar yadda mutum zai fita kasuwa yayi sana’ar sa ya dawo gidansa, kamar yadda ma’aikacin gwamnati ko ma’aikacin wani kamfani ya je yayi aikinsa ya dawo, haka na dauki fim. Na dauki fim da kyakkyawan abin yi, ban dauke shi da wata manufa ba.ina nufin sana’a na dauke shi.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Duk dan’adam ba zai rasa buri ba a rayuwa. Mun dade muna gwagwarayar nan, yanzu dai buri na a nan gaba a harkar fim bai wuce na rika furodusin ba, na rika yin fim nawa na kaina. Kuma ko zan yi wannan kafin hakan na samu miji nagari nayi aure, ina gidana zan iya yin furodusin, ko da bai bar ni na ci gaba da fim ba.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa inshaAllah.
[ad_2]
Source link