Kotu ta sahale wa EFCC ƙwace kadarorin Malami na N213bn
[ad_1]
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 na tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami na wucin-gadi.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta ce kadarorin mallakin Malami da matarsa, Asabe Bashir da ’ya’yansa biyu — Abdulziz Malami da Abiru-Rahman Malami ne, kuma tana zargin an mallake su ne ta hanyar da ba ta dace ba.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin, bayan lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho ya buƙaci hakan.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta ce an ƙiyasta darajar kadarorin za ta kai naira N213,234,120,000 da ya mallaka a jihohin Kebbi da Kano da Kaduna da Abuja.
Kotun ta ce a wallafa hukuncin ƙwace kadarorin na wucin-gadi, sannan ta yi kira ga “duk wanda da ke da alaƙa da kadarorin kuma yake ganin bai kamata a ƙwace na dindindin a miƙa wa gwamnatin tarayya ba da ya fito ya yi bayani a cikin kwana 14.”
A ƙarshe alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu domin ci gaba.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 12 bayan da kotun ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’ar da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar kotun, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
A watan Disambar da ya gabata ne ne dai Hukumar EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link