An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki

[ad_1]



Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda shida kan zargin karbar kudi daga hanun dalibai na bisa ka’ida ba.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya amince da dakatarwar.

Ana dai zargin dakatattun shugabannin makarantun ne da karɓar kudin jarabawa daga hannun daliban da suka kammala karamar sikandare (JSS) ba tare da izinin gwamnati ba, wasu daga cikinsu kuma ana zargin su sun walaƙanta shugabanni da ke sama da su.

Shugabannin da aka dakatar sun hada da shugabar makarantar mata ta Nana da Makarantar gwamnati ta Gagi (GDSS) da makarantar sakandare ta Mana da Kwalejin Giginya da Baisic ta Mana da sakandaren Silame.

Kwamishinan ya kuma kafa kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Namakka Tukur don su bincika zarge-zargen da aka yi wa shugabannin da aka dakatar.

Kwamishina, a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Muhammad Iya, ya fitar ya umarci shugabannin su mika ragamar makarantun ga hannun mataimakansu na mulki nan take.

“Ma’aikatar ilmi za ta ci gaba da yin tsayin daka ta tabbatar da tarbiya da rike amana da gaskiya a dukkan makarantun jihar Sakkwato,” a cewarsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *