Matar da ta haifi ’yan uku na neman tallafi a Yobe
[ad_1]
Wata mata mai suna Sa’adatu Abdullahi daga garin Mara cikin ƙaramar hukumar Fika a Jihar Yobe da ta haifi ‘ya’ya Uku mata biyu da ɗa namiji guda a babban asibitin ƙwararru na garin Potiskum.
Matar ta bayyana yadda take neman taimakon al’umma dangane da halin rayuwa da suke ciki ita da mijinta Abdullahi Ahmed Garin Mara.
A cewar maijegon ita da mijinta a matsayin su na masu ƙaramin ƙarfi, lalle suna fuskantar ƙalubalen ƙarancin kuɗi, yadda suke neman tallafin rayuwa daga majalisar ƙaramar hukumar Fika da kuma mutane masu karamci da ke cikin al’umma.
Ta ƙara da cewa, amma duk da matsalolin da suke fuskanta a yanzu, suna farin ciki da ƙarin iyalinsu kuma suna fatan samun taimako don taimakawa wajen ciyar da jariransu kasancewar suna cikin ƙoshin lafiya.
Don haka malama Sa’adatu ta yi kira gami da roƙo ga mazauna yankin su da kuma gwamnati da su kawo musu ɗaukin gaggawa a wannan lokaci mai cike da farin ciki, amma mai kuma cike da ƙalubalen wahalar rayuwa a gare su.
“A cewar ta gudummawa da tallafi na iya yin babban tasiri wajen tabbatar da kwanciyar hankali da wadata ga iyalanmu da ke tasowa.”
Shi ma mijin wananan mata Malam Abdullahi Ahmed garin Mara cikin bayaninsa kan wannan lamari na arzurta su da ‘ya’ya uku da Allah ya yi cewa ya yi, a gaskiya yana farin ciki da wannan albarka da Allah SWT ya azurta su da ita duk da halin matsalar rayuwa da suke ciki wadda suke neman tallafi daga gwamnati da al’umma kamar yadda matar ta sa ta ambata.
A cewarsa wannan shi ne karo na farko da suka samu irin wannan rabo na haihuwar ‘ya’ya uku lokaci guda wanda ba su taɓa tsammanin hakan ba duk da cewar kafin matar ta sa ta haihu yadda take yi na yanayin jikinta hakan kan nuna masa cewar, lalle akwai wani baƙon abu da zai faru gare ta sai kuma ga shi yadda Allah SWT Ya yi na haihuwar ‘ya’ya uku.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link