Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Bayar Da Lamba Ga Sabbin Daliban Firamare
[ad_1]
Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kaddamar da nambar da aka dauki duk dan makaranta tun daga Firamare, an yi hakan ne saboda a samu damar gane irin ci gaban da dan makaranta da ya samu domin hakan zai bada kwarin gwiwa wajen daukar ‘yan makaranta.
Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Legas, inda ya ce nan bada dadewa ba gwamnati za ta hana rubuta jarrabawa da ‘yan Firamare suke yi yayin da suka kai mizanin da za su fara karamar Makarantar Sakandare.
- Raphinha Zai Shafe Makonni 5 Yana Jinyar Raunin Da Ya Samu A Wasannin Ƙasa Da Ƙasa
- Kwankwaso Zai Koma ADC Ranar Litinin
Hakanan ma ya ce ana ta tunanin hanyoyin da za su bunkasa ciyar da yara makaranta domin ya ja hankali wajen sha’awar zuwa makarantun ta.
Alausa ya ce za’a maido da tafarkin na cikakken ciyar da yara, a makaranta ne daga ma’aikatar al’amuran jinkai ne da rage fatara zuwa ma;aikatar ilimi ta tarayya domin yadda za’a samu maida hankali sosai akan yadda lamurran su ke tafiya.
Ya ce babban dalilin da ya sa daukar matakin da yin hakan shi ne gwamnatin tarayyar tana yin hakan domin bunkasa bangaren ilimi bugu da kari kuma a samu yawan ‘yanmakaranta da suke samun gurbin zuwa karamar Sakandare daga ilimin bai daya zuwa babbar makarantar Sakandare.
Ya kara da cewa: “Muna da makarantun Firamare fiye da 50,000 a Nijeriya wadanda suke da ‘yan makaranta fiye da milyan 23.Sai dai kuma daga cikin wannan kiyasin da ake da shi fiye da milyan uku ne (3) suke samun damar zuwa kananan makarantun Sakandare.
“Tambayar ita ce, a ina saoran kusan milyan 20 wadanda basu samu damat zuwa makarantun Sakandaren gwamnti su ke? Abu mai wuya ne ace makarantu masu zaman kansu sun samy damar basu zuwa kananan makarantun Sakandare gaba dayansu.
“Magana daya ita ce rashi samun isassun wurare muna kuma aiki kan haka Akwai bukatar a gina karun makarantu don haka kuma na tattuna da kungiyar gwamnoni ta kasa dangane da hakan.Gwamnatocin Jihohi kamata ya yi su kara gina makarantu wadanda za su dauki ‘yanmakaranta da dalibai
”Domin kuma mu san irin halin da ake ciki na ‘yan makaranta da dalibai, za mu kaddamar wata namba da take ta musamman ce da zata nuna wanda yake karatu ko dan makaranta tun daga makarantar Firamare ta ‘ya’yanmu. Nambar za ta kasance mafi dacewa ga kowane dan makaranta, za kuma su kasance sun mallake ta, ba tare da la’akari da wurin da suka fara makarantar ba, ko kuma aka yi masu tiransifa ba.
“Idan dan makaranta ya kamata a kasance a ajin kamaramar Sakandare na daya ya kuma kasance baya a can, za mu san dalilin da ya sa bai ci gaba da karatun shi ba.
“Tsarin kokarin ci gaban da yaro yake samu a makaranta shi zai maye gurbin,CA yana zi iya bayyana kokarin dan makarantar tun daga aji daya na Firamare, ko da ace an maida shi zuwa wata makaranta, zai iya tafi da shi bayani yadda kokarin shi yake zuwa sabuwar makarantar.”
[ad_2]
Source link