Kwankwaso Zai Koma ADC Ranar Litinin
[ad_1]
Ana sa ran tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar ADC ranar Litinin.
Majiyoyi sun ce wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa tsakanin Kwankwaso, ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya da shugabannin ADC.
- Tsadar Fetur: Ma’aikata Da Masu Masana’antu Da Masana Tattalin Arziki Sun Nemi Daukin Gwamnati
- 2027: Ministocin Da Ake Tsammanin Za Su Yi Murabus Kafin Wa’adin Tinubu Na Ranar 31 ga Maris
A ‘yan makonnin nan, ya gana da manyan ‘yan siyasa da jagororin ‘yan adawa.
Daga ciki akwai Rauf Aregbesola, Peter Obi, Seyi Makinde, da Seriake Dickson.
Majiyoyi sun ce wannan na daga cikin ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa domin tunkarar zaɓen 2027 da kuma ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan na zuwa ne bayan rashin jituwa tsakanin Kwankwaso da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Abba, wanda ake ganin na hannun daman Kwankwaso ne a baya, ya fice daga NNPP zuwa APC tare da wasu ‘yan majalisa da masu riƙe da muƙaman siyasa a Kano.
Kwankwaso ya yi adawa da wannan mataki, inda ya bayyana shi a matsayin cin amana.
[ad_2]
Source link