Matsalar ADC Ta ADC Ce BA Ta APC Ba Ce
[ad_1]
Wannan shi ne abu na karshe da jam’iyyar (ADC) za ta so ta ji, amma dole ne a fada, ko da kuwa jam’iyyar ta ki sauraro. Lamarin ya fara ne da jinkirin rajistar jam’iyyar.
Lokacin da abubuwa ba sa tafiya da gaggawa sauya sheka na farko galibi daga jam’iyyar (PDP), lamarin da ba su zata ba sai suka zargi jam’iyyar (APC) mai mulki da jinkirta rajistar, tare da zargin cewa tana amfani da bangaren da Ralph Okey Nwosu ke jagoranta domin kara jan kafa.
- 2027: Ba Ni Da Tabbacin Samun Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa A ADC — Peter Obi
- ADC Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Saki El-Rufai Ko Ta Gurfanar Da Shi A Kotu
A karshe an yi rajistar jam’iyyar a watan Yuni. Amma hakan bai kawo karshen sabani ba. Yayin da PDP ke durkushewa kuma mambobinta da dama musamman gwamnoni suka sauya sheka, ADC ta zargi APC da lallashi, bayar da cin hanci ko kuma matsin lamba domin mayar da Nijeriya kasa mai kama da jam’iyya guda daya.
hakan na zuwa ne bayan sun gaza bayar da gamsasshiyar jujja, wadda ke cewa ko da dukkan gwamnoni a Nijeriya sun koma APC, hakan ba zai ceci jam’iyyar mai mulki daga hukuncin masu zabe mai tsauri a shekara mai zuwa ba, saboda rashin kyakkyawan aikinta.
Zaben Shugabanni
Sabuwar hujjar ita ce, jam’iyyar APC na shirin amfani da irin dabarar da ta yi amfani da ita wajen tarwatsa jam’iyyar Labour Party da kuma PDP a kan ADC: wato dasa shugaba domin raunana jam’iyyar, raba ta gida biyu, da kuma haddasa rikice-rikicen cikin gida.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ranar Litinin ta zargi jam’iyyar mai mulki da shirin amfani da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) domin amincewa da wani dan jam’iyyar da aka kora, Nafiu Bala Gombe, a matsayin shugaban kasa na ADC.
Me ya sa? “Domin tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ba tare da hamayya ba a matsayin dan takara guda daya mai karfi a takardar zabe ta 2027.”
Ban san wane irin wani sabon kulli ko zargi ADC za ta kirkiro kafin kasuwa ta gaba ba, amma ina ganin babbar matsalar jam’iyyar ita ce kanta. Idan ta ci gaba a haka, kafin APC ta kashe ta, tuni za ta riga ta mutu, kuma a kan kabarinta za a rubuta: nan ne ragowar wata jam’iyya da ta yi tunanin za ta samu mulki cikin sauki kamar ana zabar abinci daga menu!
Hanyoyin Karbe Shugabanci
Ba a ba da mulki; ana karbarsa ne, har ma a kwace shi ta hanyar tsari, shiri, da aiki. Ba a kafa jam’iyyar ADC domin ta dade ba, kamar yadda ake gina gida daga tushe, tubali bayan tubali, da hakuri a kowane mataki tare da bin tsari.
A mafi yawan lokuta, jam’iyyar hadin gwiwa ce ta masu jin haushi da kuma masu matsananciyar sha’awar mulki, bayan wasu manyan jiga-jiganta sun lalata ta ta hanyar lomawa jam’iyyar PDP.
Mun fi sanin burin zama shugaban kasa na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da Peter Obi, da kuma Rotimi Amaechi, fiye da abin da jam’iyyar take tsayawa a kai a zahiri.
Kwanan nan a Benin, Jihar Edo, an samu sabani tsakanin Odigie Oyegun da Rowland Owie, dukkansu dattawan siyasa masu shekaru da suka koma ADC, kan ko yankin Kudu maso Kudu ya kamata ya mara wa Amaechi ko Atiku baya, yayin da magoya bayan Obi ke gefe suna nuna damuwa.
Abin da ake fada da kuma aikatawa domin tabbatar da tikitin takarar shugaban kasa ga daya daga cikin ukun ya fi yawa fiye da abin da muka sani game da kokarin gina jam’iyyar.
A cikin wani yanayi da ya zama juyin akida mai muni ga asalin manufar jam’iyyar siyasa a matsayin wata cibiya, jam’iyyun sun zama kamar takardun nade-nade da ake yarwa, yayin da sauya sheka ya zama kamar wata dabara ta yaudara.
Dubi Ga Tarihi
Makomar jam’iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijeriya ta Hudu na nuna wani labari mai tayar da hankali.
Tsakanin 1999 zuwa 2015, lokacin da ludayin jam’iyyar PDP ke kan dawo, har yanzu tana iya raba ganimar siyasa ta hanyar da ta bai wa dimokuraxiyya makoma da kuma fata. Shugaba Olusegun Obasanjo ya lashe zaben shugaban kasa da kashi 62.78 cikin dari na kuri’u, rinjaye cikakke wanda ya kayar da abokin hamayyarsa Olu Falae, wanda shi ne dan takarar hadin gwiwa na jam’iyyun (APP) da (AD).
Jam’iyyar PDP ta rike jihohi 21 cikin 36, yayin da jam’iyyun APP da AD suka rike jihohi 9 da 6 bi da bi. Haka kuma PDP ta samu kujeru 59 cikin 109 na Majalisar Dattawa da kuma kujeru 206 cikin 360 na Majalisar Wakilai a wancan lokacin. Don haka abin mamaki ne ga masana tarihin siyasa cewa cikin kasa da shekaru 27 kacal na kasancewa kungiya mai karfi haka, PDP ta zama kamar ba a iya ganinta, ko da kuwa don a adana ta ne kamar gawar da aka shanya.
Tambayar, me ya faru, tana samun amsa mai sauki amma mai dacewa, wato dora laifi kan Tinubu, duk da cewa tsutsar da ke cin ‘yan adawa tana cikin ‘yan adawar ne da kansu.
Tuna Baya Shi Ne Roko
Bayan zaben gama-gari na 2023, PDP, ragowar da daga ciki da yawa daga mambobin ADC suka fito ta samu kujerun gwamna 10: Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Delta, Enugu, Oyo, Filato, Rivers, Taraba, da Zamfara, yayin da ta 11 ita ce Bayelsa a zaben da aka yi a lokacin da ba cikakken zagaye ba. Wannan ya isa don bai wa jam’iyyar damar fafatawa, idan shugabanninta suna da gaskiya.
Manyan jam’iyyun da suka haifa su ne APC (ACN, CPC, da ANPP), wadanda suka kayar da PDP a 2015 tare da taimakon wasu gwamnonin da suka tsere daga PDP, sun rike jihohi 11 kacal. A gaskiya, bayan zaben 2003, Lagos ce kawai jiha ta AD a Kudu maso Yamma, sauran jihohi biyar kuwa PDP ta cinye.
Amma a kidayar karshe, PDP ta rasa tsofaffin matsugunninta na karfi a Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas, da Arewa Tsakiya saboda ambaliyar sauya sheka. Gwamnoni da ke kallon sake zabe da wasu da ke neman ritaya mai dandano zuwa Majalisar Dattawa kusan gaba daya sun bar PDP kamar masu sauka daga jirgi mai fadowa.
A cikin wani yanayi mai tsanani na juyin kaddara, jam’iyyar ta zama wacca kaddara ta shafa saboda mugun misalin da ta kafa a harkar siyasa, inda babu sakamako ga wadanda suka tsere daga jam’iyya ko suka shiga, suna dauke da kujerunsu tare da su.
Daga cikin gwamnonin 11 a watan Mayu 2023, biyu kacal Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde na Oyo ne suka rage a bangaren PDP.
Mohammed, wanda ya yi kokari sosai wajen jan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan cikin zaben shugaban kasa na 2027, ya ga mafarkinsa ya rushe yayin da jam’iyyar ke rugujewa a cikin rikice-rikicen shari’a, sauya sheka, da rikicin iko. Kuma jita-jita na cewa Bala na kan kusurwar barin duk abin da ya rage na tagwayen PDP tare da Makinde nan ba da jimawa ba.
Kula Da Yadda Abubuwa Ke Tafiya
Halin da ake gani a fadin Nijeriya gabadaya yana nuna sakamakon daya a zaben gama-gari na shekara mai zuwa nasara ga jam’iyyar APC mai mulki. Ba saboda kyakkyawan aikin da ta yi ba, sai don saboda ‘yan adawa, musamman ADC, sun shimfida tsari ta hanyar sanya kansu ba a matsayin madadi don canji ba, amma a matsayin wuri inda ‘yan siyasa kadan masu matsananciyar sha’awar mulki ke fafatawa.
Ina dariya duk lokacin da ADC ke kiran kanta jam’iyyar adawa. Kusan tana adawa ne. Za ka yi mamaki ka san cewa wani babban jigon ADC yana sadaukar da kansa ga manyan shugabannin APC domin kare muradunsa na kasuwanci da ke cikin hadari.
Tantance Tarihi
A karshe, babban abokin adawar APC zai kasance APC kanta. Wannan shi ne darasin tarihi. Daga Jam’iyyar Conservative ta Birtaniya zuwa Indian National Congress, kuma daga African National Congress zuwa ragowar PDP ta Nijeriya (wadda nan ba da jimawa ba za ta dauki Tinubu a matsayin dan takararta), tarihi ya nuna cewa jam’iyyun da ke mulki akarshe suna lalacewa da raguwa daga cikin kansu.
Hadewar rashin kulawa, rarrabuwar cikin gida, da gazawar daidaitawa da sabbin yanayi na jama’a, ko cin hanci da rashin dabi’a mai kyau, a karshe yana shafar su kuma ya rinjaye su.
Halin APC ba zai bambanta ba, ba saboda hayaniyar da ADC ke yi ba.
Ishiekwene shi ne Babban Editan jaridar LEADERSHIP kuma marubucin littafin Writing for Media and Monetising It.
[ad_2]
Source link