Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa
[ad_1]
Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba.
Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita.
Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata cewa dakatarwar da aka yi mata ba ta dace ba, sannan ta umarci majalisar da ta mayar da ita bakin aiki.
Sai dai a wata wasiƙar martani da majalisar ta aika wa Sanatar a ranar 4 ga Satumba mai dauke da sa hannun muƙaddashin Akawun Majalisar, Yahaya Danzaria, ta ce ba za ta koma bakin aiki ba har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu.
Ya ce: “Wannan maganar tana gaban kotu, kuma majalisar ba za ta yi komai a game da batun komawarki bakin aiki ba har sai an kammala shari’ar baki ɗaya. Don haka, a yanzu babu abin da ofishinmu zai iya yi a game da wannan batu.”
Idan ba a manta ba tun a ranar 6 ga watan Maris ne dai Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha, bayan wata musayar yawu da ta yi da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link