TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur
[ad_1]
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki dangane da matakin da Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ɗauka na ƙara harajin kaso 5 cikin 100 a farashin duk litar man fetur.
A yayin da ƙungiyar ta yi watsi da matakin, ta kuma kwatanta aiwatar da hakan a matsayin ganganci da mugunta ga tattalin arzikin ƙasar.
A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayyar ta sanar da ɗaukar wannan mataki da zai fara aiki a farkon watan Janairun 2026, domin samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen gina hanyoyi da sauran manyan ayyuka a ƙasar.
Sai dai tuni ƙungiyar ta TUC ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki 14 da ta janye wannan matakin, ko kuma ta ɗauki matakin da take ganin ya dace.
A cewar, ƙungiyar ƙwadagon, cikin matakin da za ta ɗauka har da rufe manyan sassan gwamnati musamman masu samar da kuɗaɗen shiga.
Wata sanarwa da Festus Osifo da kuma Nuhu Toro, shugabannin ƙungiyar suka sanyawa hannu, sun ce a halin da ake ciki ’yan Najeriya na cikin ƙangin biyan haraje-haraje barkatai.
Shugabannin ƙungiyar ƙwadagon, sun ce sabon harajin ba abu ne da zai yiwu ba, don haka ya zama wajibi gwamnati ta dakatar da shi.
A cewarsu, har yanzu ’yan Najeriya ba su gama farfaɗowa daga ƙangin da cire tallafin man fetur ya jefa su ba, baya ga lalacewar darajar Naira.
Kazalika, ƙungiyar ta ce ta fara sanar da sassanta na jihohi don shirin tafiya yajin aiki, idan hakan ta kama.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link