Kirsimeti: Gwamnan Gombe Ya Karɓi Baƙuncin Kiristoci

[ad_1]

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da rungumar zaman lafiya, da ƙauna da haƙuri da juna a matsayin ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin al’ummar Kirista da suka kai masa gaisuwar Kirsimeti a Fadar Gwamnati da ke Gombe.

Ya taya Kiristoci a jihar da faɗin ƙasar nan murnar bikin Kirsimeti, yana mai bayyana lokacin a matsayi na tunatar da muhimmancin ƙauna, da sadaukarwa, da haɗin kai da zaman lafiya. Gwamna Yahaya ya jaddada cewa Jihar Gombe ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na rarrabuwar kai bisa addini ko ƙabilanci ba.

  • Mutane 7 Sun Mutu, 4 Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Mota A Yobe
  • Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Ina taya ƴan’uwanmu Kiristoci murnar Kirsimeti. Zaman lafiya shi ne ginshiƙin duk wani ci gaba, kuma dole ne mu kiyaye shi domin makomar jiharmu da Nijeriya baki ɗaya,” in ji gwamnan, yana mai gargaɗi kan aiyukan masu son tayar da zaune tsaye.

A nasa jawabin, Shugaban CAN na Jihar Gombe, Rev. Joseph Alphonsus Shinga, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan shugabancinsa na damawa da kowa da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya. Al’ummar Kirista sun bai wa gwamnan kyautar Kirsimeti, yayin da shi ma ya tallafa musu da kyaututtuka domin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *