Rikicin Dangote da Shugaban NMDPRA ya dauki sabon salo

[ad_1]



An sake sa zare tsakanin Shugaban Kamfanin Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Dangote, da Shugaban Hukumar kula da Harkokin Mai da Kasuwancinsa ta Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.

Ɗangote ya zargi shugabancin hukumar da daƙile ƙoƙarin bunƙasa tace man fetur a cikin gida a Najeriya.

A wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Lahadi a matatar, Dangote ya ce ana amfani da shigo da man fetur daga waje ne domin dakile karfin da ake da shi a cikin gida, lamarin da ke samar da ayyukan yi a kasashen waje yayin da ’yan Nijeriya ke fama da kalubalen masana’antu.

“Ba za ka yi amfani da shigo da kaya daga waje ka dakile karfin cikin gida ba,” in ji shi. Ya kara da zargin cewa shugabancin NMDPRA na tauye tace man fetur a cikin gida ta hanyar ci gaba da bayar da lasisin shigo da kayayyakin man fetur, “duk da karuwar karfin tacewa a cikin gida.”

A cewarsa, wadannan matakai na hukumar sun kara jefa Nijeriya cikin dogaro da shigo da mai tare da hana masu zuba jari sha’awar yin hakan a fannin tacewa a cikin gida.

Dangote ya kuma bukaci a binciki Babban Daraktan NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, inda ya yi ikirarin cewa an bayar da lasisin shigo da kusan lita biliyan 7.5 na man fetur domin zangon farko na shekarar 2026, a daidai lokacin da masu tacewa na cikin gida ke fama da rashin riba.

Ya kuma zargi Injiniya Ahmed da rayuwa fiye da yadda kudaden halal dinsa suka dace, yana mai nuni da ikirarin cewa ’ya’yansa hudu na karatu a makarantun sakandare a Switzerland, kan kudin da ya kai miliyoyin daloli.

“Ba na neman a cire shi daga mukaminsa ba, sai dai a yi cikakken bincike,” in ji Dangote, yana mai cewa, “Ya kamata a tilasta masa ya yi bayani kan ayyukansa tare da tabbatar da cewa bai yi amfani da mukaminsa ta hanyar da za ta cutar da ’yan Nijeriya ba.”

Ya bukaci Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) da sauran hukumomin da suka dace su binciki lamarin, yana mai cewa a shirye yake ya gabatar da hujjoji don tabbatar da ikirarin nasa idan aka kalubalance shi.

Dangote ya yi gargadin cewa ci gaba da shigo da man fetur da aka riga aka tace na cutar da samarwa a cikin gida tare da jefa kananan matatun mai cikin barazanar rugujewa. Ya kuma soki abin da ya kira “tsattsauran muradun wasu bangarori” da ke cin gajiyar shigo da man fetur, a kan asarar ci gaban kasa.

Dangane da farashi, Dangote ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa farashin litar man fetur zai kara sauka, daga ranar Talata, zuwa N740, farawa daga Legas, bayan rage farashin gangar matatar zuwa N699 kowace lita. Ya ce gidajen man MRS ne za su fara aiwatar da sabon farashin.

Ya ƙara da cewa matatar ta rage adadin mafi karancin siye da ake bukata domin bai wa karin ’yan kasuwa damar shiga, kuma tana shirye ta tura manyan motocin gas ɗin CNG a fadin kasar domin tabbatar da sauƙin farashi.

Ɗangote ya jaddada cewa a karshe ’yan Nijeriya ne za su amfana da tace man fetur a cikin gida, koda kuwa masu shigo da shi daga waje suna fuskantar asara.

Ya sake nanata shirin sa na sanya hannun karin Matatar Dangote a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya domin bai wa ’yan Nijeriya damar mallakar hannun jari a matatar. “Wannan matatar ta ’yan Nijeriya ce da farko. Ba zan ja da baya ba,” in ji shi.

Har zuwa lokacin buga wannan labari, babu wata sanarwa ta hukuma daga NMDPRA kan zarge-zargen. Da aka tuntubi kakakinta, George Ene-Ita, ya ce ba shi da wata magana a kai.

Rikicin Dangote da Farouk a NMDPRA

Tun bayan fara aikin Matatar a watan Janairun 2024, Dangote ya shiga taƙaddama mai tsawo da NMDPRA.

Rikicin ya fara ne a watan Yulin 2024, da Babban Daraktan NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya ce kayayyakin da matattun cikin gida ke samarwa, ciki har da na Dangote, ba su kai ingancin wadanda ake shigo da su daga waje ba.

Ya bayyana cewa matatar tana matakin kafin kaddamarwa gaba daya ne kuma ba ta da cikakken lasisin aiki, yana zargin Dangote da neman mamaye kasuwar samar da man fetur a Najeriya.

Ɗangote ya karyata zarge-zargen rashin ingancin, lamarin da ya sa Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike tare da kiran a dakatar da Ahmed daga aiki.

A watan Agusta, NMDPRA ta dage kan cewa matatar har yanzu tana matakin kafin ƙaddamarwa, kuma ba a ba ta lasisin aiki ba.

A watan Oktoban 2025, tawagar Ahmed ta ce NMDPRA ta ba wa matatun cikin gida damar samar da dizal mai kayyadadden sinadarin sulphur har zuwa Janairun 2025, bisa amincewar ECOWAS.

Sai dai gwaje-gwajen da Ɗangote ya jagoranta sun nuna cewa dizal dinsu na ɗauke da sulphur mai matukar ƙaranci, saɓanin ikirarin da aka yi a baya.

A wancan lokaci, Majalisar Wakilai ta ce dole a dakatar da Shugaban NMDPRA kan kalamansa na cewa dizal ɗin Dangote na ɗauke da sulphur mai yawa, har sai an kammala bincike.

An dauki wannan matsaya ne bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisa Esosa Iyawe ya gabatar. Yayin gabatar da kudirin, ya tuna cewa shugaban NMDPRA ya ce dizal ɗin Dangote ya fi na waje muni, yana ɗauke da sulphur tsakanin 650 zuwa 1,200 ppm.

Ya ce: “Dangote a matsayin kariya ya nemi a gwada kayayyakinsa, inda ’yan Majalisar Wakilai suka sa ido, kuma aka gano cewa dizal dinsa na dauke da sulphur 87.6 ppm, yayin da samfurorin dizal biyu da aka shigo da su daga waje suka wuce 1800 ppm da 2000 ppm bi da bi, wanda ya ƙaryata zarge-zargen shugaban NMDPRA.

“An kuma yi zargin cewa NMDPRA na bai wa wasu ’yan kasuwa lasisin shigo da dizal mai ɗauke da sulphur mai yawa, wanda amfani da shi ke haifar da babbar barazana ga lafiya da kuma asarar kuɗaɗe ga ’yan Nijeriya.”

Fara da NNPCPL

Dangote ya kuma taba yin taƙaddama da tsohon shugabancin NNPCL ƙarƙashin Mele Kyari, inda ya zargi tsohon shugaban na NNPCL da tafiyar da matatar man fetur a kasar Malta.

“Wasu daga tashoshin, wasu mutanen NNPCL da wasu ’yan kasuwa sun buɗe matatar man fetur a wani wuri kusa da Malta. Mun san waɗannan wurare, mun san abin da suke yi,” in ji Ɗangote.

Kyari ya musanta zargin, yana mai cewa bai san wani ma’aikacin NNPCL da ke da ko ke tafiyar da irin wannan matata a Malta ko a wani wuri ba. Sai dai ya ce irin waɗannan matatun ba su da tasiri kan harkokin kasuwanci da tsare-tsaren NNPCL.

Bayan nada sabon Shugaban Kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, rikicin matatar da kamfanin ya ragu.

Dalilin tsauraran kalaman Ɗangote

Yyayin da Ɗangote ke nanata cewa matatarsa na iya biyan bukatar cikin gida, NMDPRA na ci gaba da nuna saɓanin haka.

Misali, a ranar 31 ga Oktoba, matatar ta bayyana cewa yanzu tana fitar da lita miliyan 45 na fetur da lita miliyan 25 na dizal a rana, tana mai jaddada kudurinta na tabbatar da wadataccen samarwa a fadin kasar.

Kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya ce karfin samarwar su yanzu ya zarce bukatar cikin gida.

Kalaman Ɗangote sun zo ne kwana guda bayan amincewa da sanya harajin kashi 15 cikin 100 kan shigo da fetur, dizal da man jirgi, lamarin da ya jawo ra’ayoyi mabanbanta.

Yayin da wasu masana tattalin arziki suka yaba da matakin a matsayin kariya ga matatun cikin gida, wasu manyan ’yan kasuwa sun yi adawa, suna gargaɗin cewa zai iya haddasa karin farashin mai. A karshe dai an janye tsarin.

Duk da kasancewar Matatar Ɗangote da ta fara aiki sama da shekara guda, shigo da man fetur daga waje na ci gaba, inda kusan kashi 67 cikin 100 na buƙatar yau da kullum ake shigo da shi, yayin da Ɗangote ke cewa matatarsa mai karfin gangar 650,000 a rana na iya biyan bukatar cikin gida.

NMDPRA ta ƙalubalanci alƙaluman Ɗangote

Duk da fitar da alkaluma da bayanai da dama daga Dangote, bayanan NMDPRA na nuna akasin haka.

A farkon Disamba, NMDPRA ta ce matsakaicin lita miliyan 71.5 a rana na PMS aka samar a watan Nuwamba, sama da lita miliyan 46 na Oktoba.

Sai dai bayanai sun nuna cewa lita miliyan 52.1 a rana an shigo da su daga waje, yayin da lita miliyan 19.5 ne aka samar a cikin gida daga Matatar Dangote.

Majalisar Wakilai ta shiga tsakani

Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar dokoki ta ƙasa kan albarkatun man fetur ya gayyaci bangarorin biyu domin gabatar da koke-kokensu, tare da umartar su dakatar da musayar kalamai a kafafen yada labarai har sai an kammala bincike.

Shugabannin kwamitin, Ikenga Imo Ugochinyere da Henry Okogie, sun bayyana hakan bayan taron gaggawa.

Kwararren mai da gas, Daga Marcel Okeke, ya goyi bayan bukatar binciken NMDPRA, yana mai cewa hakan na da muhimmanci ga gaskiya da rikon amana.

Haka kuma, Dakta Ayodele Oni ya ce shigo da mai daga waje ana yi ne don cike gibi idan samarwa a cikin gida bai wadatar ba.

Farfesa Wumi Iledare, Masanin Tattalin Arzikin Man Fetur, ya bayyana cewa abin da ake gani ba rikici ba ne, sai dai sauyin tsari a kasuwar man fetur ta kasa, sakamakon shigowar Matatar Dangote.

Daga Sagir Kano Saleh, Itodo Daniel Sule & Faruk Shuaibu (Abuja) & Abdullateef Aliyu (Legas)


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *