Kotu ta ɗage shari’ar BBC Hausa da mawaƙi Abdul Kamal zuwa Sabuwar Shekara
Kotu ta ɗage sauraron shari’ar haƙƙin mallakar sautin kiɗa da wani maka Sashen Hausa na BBC a gabanta a Jihar Kano.
Mai shari’a Muhammed N. Yunusa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya sanya 10 ga Fabrairu a matsayin ranar ɓangarorin da ke Shari’a za su gabatar da jawaban ƙarshe a rubuce kan ƙarar da mawaƙi a Kano, Abdul Kamal, ya shigar da Sashen Hausa na BBC.
Mawaƙin yana tuhumar BBC Hausa da amfani da sautin waƙarsa a cikin ɗaya daga shirye-shiryensu mai suna “Daga Bakin Mai Ita” ba tare da izininsa ko amincewarsa ba.
Haka kuma, yana roƙon kotu ta tilasta wa kamfanin watsa labaran biyan sa diyya ta miliyan 120.
A zaman kotun da aka ci gaba da sauraron shari’ar, BBC ta gabatar da shaidarta ta uku, Jamilu Musa, wani mai tsara kiɗe-kide, wanda a cikin shaidarsa ya ce shi ne ya samar da sautin waƙar da ake magana a kai.
Musa, wanda lauyan BBC AbdulShakur ya jagoranta wajen bayar da shaida, ya bayyana faifan flash drive da ya adana sautin waƙar da ya samar wa BBC, bayan haka lauyan ya nemi a kunna sautin a gaban kotu, kotun kuma ta amince.
Sai dai a yayin masa tambayoyi daga lauyan wadanda aka yi ƙara, Bashir Ibrahim Umar, mai ba da shaidan ya ce ba a rubuta sunan BBC a kan rasidin biyan kuɗi N110,000 da ya bayar ba, yana mai jaddada cewa ya samar da tarin sautin waƙoƙi da dama ga BBC, kuma bai san Abdul Kamal ba.
BBC ta kammala kare kanta a shari’ar bayan gabatar da shaidarta ta uku.
Dukkan ɓangarorin, wato BBC da Kamal, za su gabatar da jawaban ƙarshe a rubuce zuwa ranar da aka ɗaga shari’ar a cikin watan Fabrairu, domin bai wa kotu damar yanke hukunci.