Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse

[ad_1]



Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19.

Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya.

Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma.

Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba.

“Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan su ɓace bayan sun yi nasara,” in ji Yakubu Ayuba, mazaunin Talasse.

Ya ce rashin wuta ya jawo durƙushewar kasuwanci da tattalin arziƙi a yankin, kuma hakan zai yi tasiri a zaɓen 2027.

Wani mai sana’ar ɗinki, Musa Adamu Galadima, ya ce: “Janerata ya fi ƙarfinmu. Na kori yaran da ke koyon sana’a saboda ba zan iya ɗaukar nauyinsu ba.”

Shi ma Sulaiman Idris, mai sayar da lemun kwalba, ya ce yana kashe kusan Naira 10,000 a rana wajen siyan ƙanƙara.

“Lokacin da aka kawo kayan aiki mun yi farin ciki, amma yanzu komai ya tsaya,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi ɗan majalisar don jin ta bakinsa, Ali Isa JC, ya ce matsalar ta samo asali ne daga jinkirin sakin kuɗaɗen aikin daga Gwamnatin Tarayya, amma suna ƙoƙarin ganin aikin ya ci gaba.

A halin yanzu, gwamnatin Jihar Gombe ta fara aikin samar da wuta ta hanyar samar da ƙaramar madatsar ruwa da hasken rana a Dam ɗin Balanga, wanda zai iya samar da 620KW.

Duk da haka, jama’ar Talasse sun ce rashin wutar zai sa su ƙauracewa kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *