An Nuna Bidiyon Gabatarwar Shirye-Shiryen Bikin Bazara Na CMG A Afirka Ta Kudu

[ad_1]

Kwanan nan, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na 2026 na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a Suncity, sannanen wurin yawon bude ido ne na Afirka ta Kudu.

Bayan watsa bidiyon tallatawa na farko a shekarar 2025, bana ita ce shekara ta biyu a jere da aka gabatar da bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na kasar Sin na CMG ga masu yawon bude ido na duniya a nan.

An wallafa bidiyon kan allon talla dake wurin yawon shakatawar, abubuwan dake alaka da al’adun Sin dake cikin bidiyon na ci gaba da jawo hankulan masu yawon bude ido na kasashen duniya inda da dama suke tsayawa suna kallo.

Bugu da kari, an sake nuna bidiyon a gun bikin murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa da aka yi a Zambia, kuma an nuna shi a liyafar maraba da bikin bazara na ofishin jakadancin kasar Sin da ke Antigua and Barbuda da kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake Rasha. Haka kuma ya fara bayyana a filayen manyan gasannin wasan kwallon kafa guda biyar na yankin Turai a karon farko.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *