Tinubu Ya Bada Sabbin Umarni Ga Shugabannin Sojoji

[ad_1]


Shugaba Bola Tinubu ya bayar da sabbin umarni ga Shugabannin Sojojin Nijeriya da shugabannin hukumomin leken asiri a wani bangare na kokarin inganta yanayin tsaron kasar.

Shugaba ya gana da shugabannin tsaron a ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, a wani zaman sirri da ya dauki sama da awa daya.

Da yake jawabi bayan taron, Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede, ya ce, Shugaban ya bayar da sabbin umarni da nufin cimma sakamako mafi kyau a yaki da rashin tsaro.

A cewarsa, hukumomin tsaro yanzu suna inganta hadin kansu kuma sun kuduri aniyar tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun yi bukukuwan Kirismati da na karshen shekara cikin aminci da kwanciyar hankali.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nada tsohon CDS, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro bayan murabus din tsohon Minista, Mohammed Badaru Abubakar, a ranar Litinin.

Masu sharhi na cewa, duk hakan na nuna fatan Shugaban wajen ganin an daidaita tsarin tsaron kasar da nufin samun sakamakon da ake fata.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *