An Kashe Manjo Da ‘Yan Ta’adda 10 A Hare-haren Da Aka Daƙile Kan Sansanonin Soja

[ad_1]

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta ‘Joint Task Force, JTF’ (Arewa maso Gabas), wato Operation Hadin Kai, sun dakile hare-hare da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka kai kan sansanonin soji na gaba-gaba (Forward Operating Bases), FOB da ke Mayanti, Gajigana da Gajiram a Jihar Borno tsakanin ranar 28 ga Fabrairu zuwa 1 ga Maris, 2026.

A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar JTF (Arewa maso Gabas), Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya sanya wa hannu, rundunar sojin ta ce an samu nasarar daƙile hare-haren.

  • Gwamna Dauda Ya Yaba Da Yadda Aiki Ke Tafiya A Babban Filin Wasa Na Gusau
  • Kasar Sin Na Adawa Da Yin Amfani Da Karfi A Huldar Kasa Da Kasa

A cewarsa, sansanin FOB Mayanti ya fuskanci mummunan hari a ranar 28 ga Fabrairu, inda dakarun suka dakile harin, inda suka gano gawawwakin ‘yan ta’adda biyar bayan artabun.

An sakw kashe ‘yan ta’adda uku a Gajiram, da biyu a harin Gajigana.

Uba ya kuma tabbatar da cewa an kashe wani babban jami’in soja guda ɗaya a yayin artabun.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *